Ba na tunanin samun kamar ki domin raina gabaɗaya ya kamu da son ki. Na sani cewa zan yi alfahari da ke idan kika furta kalmar ina son ka a matsayin amsar ki gare ni.
Marubuci: Imran Musa Jahun
Lambar yabo a gare ki mai sona.
Zinariya masoyiyar raina.
Gimbiya alkhairin rayuwata.
Sarauniya cikon farin cikina.
Tauraruwa hasken ruhina.
Lokaci ɗaya rurutaccen son ki ya ruru a zuciyata, sai dai sanin cewa ke wata daban ce cikin 'yammata, ma'ana ke tamkar sarauniyar su ce, shi ya sanya na miƙo gaisuwar ban girma a gare ki sahibata.
Ina son ki da wani irin so mai ɗauke da sinadarin ratsa dukkan sassan jiki. Ke ɗaya ce mafi haske da dawwama a zuciyata. Ina son ki.