Idan kika sanya soyayya ta a cikin zuciyar ki kin gama mini komai a rayuwata, bayan ke ba zan ba da kaina ga kowacce 'ya mace ba. Ke ce ɗaya tilo a cikin ƙalbina da ba za ki canzu ba.
Marubuci:- It'z Nazeephancy DH
Ina jin ki a kowanne irin yanayi da lokaci, safiya da maraice rana ko hantsi ki haɗa har da dare. Barka da lokacin sanyi.
A cikin baccina ko a farke kodayaushe gizo kike mini, saboda ƙaunar ki tana a tare da ruhina.
Aikin yabon kyawawan ɗabi'unki da kyawawan halayen ki su ne aikin da zuciyata ba ta gajiyawa da yin su a kodayaushe.
Ke ce farin cikina. Kuma ke ce baƙin cikina, tunani nake idan ba ke ina zan sa kaina? domin duk wata kulawa da nake buƙata to daga gare ki ne kawai nake buƙata.
Ki ɗan ba ni guri na zauna domin huce duk gajiyar da na kwaso akan hanya ta ta zuwa sansanin masoyan ki. Zan so a ce na zama shugaba, jagaba, jagora, limamin cikin su, idan hakan ba ta samu ba to Don Allah kar ki kai ni ƙasa da muƙamin na'ibi.
Fatana ki ji kin gamsu da duk abin da na faɗa cewa gaskiya ne. Kuma ki amince.
Kuma ki yarda da ni ki ba ni damar hawa kan sahun masoyan ki.