Saturday, 14 December 2024

Gajerun Kalaman Soyayya Na Nuna Tsantsar Farin Ciki Ga Masoyiya

Tura Wannan Zuwa Ga

Ki yi murmushi don faranta raina, ki yi dariya don ki sani farin ciki, tabbas soyayyarki ta zamar mini garkuwa a zuciyata.


Gajerun Kalaman Soyayya Na Nuna Tsantsar Farin Ciki Ga Masoyiya
Hoto: Prostock-studio/Shutterstock

Marubuci:- Abubakar Usman


Ba ni da wani buri wanda ya wuce na rayu da ke har ƙarshen numfashina.


Ke ce wacce nake so nake matuƙar ƙauna.


Ke ce farin ciki na.


Ke ce walwalata.


Ke ce nishaɗina.


Ke ce mahaɗin rayuwata.


Ya zan yi idan kika bar ni?


Ke ce tauraruwar da ke haskaka duhun zuciyata.


Ke ce sarauniyar da ke mulkar birnin zuciyata.


Ke ce zinariyar da ke ƙawata zuciyata.


Ke ce gimbiyar da ke kula da fadar zuciyata.


Ke kyakykyawa ce, kuma fitacciya a cikin mata.


Masoyiyata mahaɗin rayuwata, ki aminta da soyayyata domin na samu sauƙin ƙunar da ke cikin zuciyata. Ni ne naki.


Ganin ki a kusa da ni shi ne ke ƙarfafa mini zuciyata ya sani farin ciki.


Son da nake miki ya wuce kwatancen masu kwatance.


Kin riga da kin zama ni, jinin jikina ya riga da ya ƙare, soyayyarki ita ce ke yawo a jikina, rashin ki na iya sanadiyyar rasa rayuwata.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user