Wednesday, 4 December 2024

Gajerun Kalaman Soyayya Na Rana

Tura Wannan Zuwa Ga

A ce na kasance a tare da ke a kowanne irin yanayi da lokaci cikin samun kulawarki ta musamman, to na san dawwama zan yi cikin farin ciki da walwala da annashuwa mai yalwa da ƙawatuwa waɗanda ba za a iya misaltawa ba.


Gajerun Kalaman Soyayya Na Rana
Hoto: Netfalls/Dreams time

Marubuci:- It'z Nazeephancy DH


Da na ce "Ina son ki". Ba wai fa ina nufin ina son ki ba ne kawai. Ina nufin ina ƙaunar ki ne. 


Irin ƙaunar nan wacce take kasancewa a tare da ruhi a safiya da rana da maraice haɗa da yammaci da darare, a koyaushe soyayyar ki da ƙaunar ki su ne ababen duniya mafi kusanci da numfashina.


Ni kam idan na rasa ki ban san yadda rayuwata za ta koma ba.


Cikin ɗan ƙanƙanin lokaci kika mallake ni ni da komai nawa, zuciyata, rayuwata, dukiyata, nutsuwata, tunanina, nazarina da sauransu.


A yanzu babu abin da ya rage a gare ni face tarin son kasancewa abokin rayuwar ki.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user