Kallon kyakykyawar fuskarki mai cike da annushuwa ya kan ƙaramin ƙarfin gwiwa da jarumtar da za su sa na ji kamar zan iya yaƙar duniya.
Gajerun Kalaman Soyayya Na Saida Safe
Hoto: Wallup
Marubuci:- Rabs
Kin kasance tamkar dukkanin wani motsina, a kullum idan ban saki a idona ba sai na kasance tamkar mara lafiya.
Soyayyarki ruwan zuma ce a gare ni da zan sha domin warkar mini da wata cuta.
Zuciyata tamkar wani fage ne da yake cike da soyayyarki, na kasance a kullum ba ni da wani abu muhimmi wanda ya wuce tunaninki. Ina son ki rayuwata, ruhina, muradina, murmushina saida safe tawan.