Ina fatan ba za ki zarge ni ba, ko kuma ki damu idan na kira ki da likitar zuciyata ba, wadda ke ba ta kulawa ta musamman a duk lokachin da ta kamu da cututtukan so. Ina son ki.
Marubuci: Abba Rabi'u Matallawa
Zan sanar da ke ke kuma ki taya ni isarwa zuwa ga duk wani wanda ke tantamar soyayyarmu cewa ni da ke tamkar jiki da ruhi ne ɗayansu ba zai yi cikakkiyar rayuwa ba sai da ɗayan, soyayyarmu kuwa kamar zanen dutse take.
Dukkanin kalmomin da nake faɗa miki a yanzu da kuma sauran lokuta na baya su ne zahiri, baɗininsu yana can cikin fadar zuciyata sai na zama ke ke ma kin zama ni sannan za ki fahimce su. Ke ta musamman ce a gare ni.
Ni da ke matafiya ne waɗanda tafiyarsu ke gudana cikin gungun 'yan adawa, ki kau da kai daga dukkanin maganganun maƙiyanmu a kaina. Kowanne matafiyi akwai wajen da ya nufa, ni da ke muna kan hanyar zuwa dandalin masoya ne domin cika ƙudurin mu na shiga ɗakin aure.
Idan har kuna jin daɗin maƙalolin shafin nan namu, to ku hanzarta sanar da dukkan abokan ku ko ƙawayen ku da dukkan waɗanda ku sani, ku gaya musu sunan adireshin shafin nan namu domin su ma su shigo cikin shafin su dinga amfana da shi kamar yadda ku ma kuke yi a kullum a kyauta.