Gari ya waye hasken alfijir ya keto, tsananin sanyin safiya da iska duk suna kaɗawa.
Marubuci:- Sadik Ebra
A lokacin da zakaru ke cara, a lokacin da yabon ki, begenki da tsananin ƙaunarki ke ƙara kutsawa cikin zuciyata.
Da soyayyar ki nake kwana da ita nake tashi, a duk bugun numfashina ke ce halittar da nake tunawa, samun ki a kusa da ni shi ne burin zuciya da sauran sassan jikina.
Na fi son a ce na same ki domin gusar da duk wani hijabin baƙin cikin zuciyata, ke kaɗai ce ke wanzar da sanyin zuciya da kwanciyar hankalina.
Wani lokacin sai na kasa zaune na kasa tsaye, ke kawai nake tunawa, ya abar alfaharina.