Friday, 13 December 2024

Har Yanzu Kana Damuwa Da Mayaudara ko Macuta?

Tura Wannan Zuwa Ga

Duk wanda ya cuce ka, ya riga ya cuce ka, la'alla ma ya manta da kai a tarihin rayuwarsa, me yasa kai ma ba za ka yi hakan ba? Shin tsakanin kai (mutumin kirki) da shi (mayaudari) wane ne ya fi kamata ya kasance cikin farin ciki?


Har yanzu kana damuwa da mayaudara ko macuta?
Hoto: Queenmoonlite Studio/Freepik

Marubuci:- Abdulfatah Yakubu


Mafi girman abin da za ka ɗauka bayan cutar macuci shi ne darasi, amma kada wannan darasin ya hana ka mu'amalantar mutane kamar yadda ka saba.


Duniya faɗi gare ta, halayya da ɗabi'un mutanen cikin ta sun bambanta, ka saki jiki ka yi rayuwar ka, ka ƙwanƙwasa ƙofa domin tarayya da mutanen ƙwarai. Sannan ka buɗe zuciyar ka domin karɓar farin cikin da yake tattare da su.


Ba a sarin mumini sau biyu a rami ɗaya, duk wanda ka ga tarihi ya maimaitu a kansa to ɗayan biyu ne, kodai bai ɗauki darasi da kyau ba, ko kuma wannan darasin da ya ɗauka ya hana shi buɗewa mutanen ƙwarai zuciyar sa.


Ka ɗauki darasi, ka sarrafa wannan darasin ta hanyar da ta dace.


Rayuwa ce, da sannu za ka goge watarana.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user