Yawaita tunani babbar matsala ce ga rayuwar Ɗan Adam, yana jawo abubuwa da dama, da ƙalubale mai yawa, ya kan sanya mutum shakka kodayaushe akan duk abin da yake rayuwa akai, kodayaushe zai dinga rayuwa ne a bisa munanan tunane-tunane, tsoron yin kuskure, wahalar ɗaukar mataki ko yanke shawarar da ta dace, kasa mantawa da matsaloli wanda yake dawwamar da mutum a cikin yanayin baƙin ciki, wanda hakan ba ƙaramar matsala zai jawo ba, kamar kasancewa cikin damuwa, da rashin walwala,rashin kyakkyawar alaƙa, rasa damarmaki, mafi muhimmanci shi ne yawaita tunani shi ne babban abin da yake jawo baƙin ciki, rashin walwala, damuwa, da kuma dawwamar da su a rayuwar Ɗan Adam, wanda su kuma su kan jawo matsaloli masu yawa da ba za su ƙirgu ba, idan aka lazimce su, matsalolin za su iya kasancewa ga lafiya, rayuwa, mu'amala da ma kowanne ɓagare na rayuwa.
Marubuci:- Ibraheem Aleeyu
Waɗannan wasu hanyoyi ne da za su taimaka maka wajen sambaɗe yawan tunani a rayuwar ka, kamar haka:
Matsaloli
Ba kasafai matsaloli su kan zama matsala ba: Sau da yawa abubuwan da kake ganin su a matsayin matsaloli, ba matsala ba ne, kaso 99% na abubuwan da kake ganin su a matsayin matsala kai ne kawai ka ƙirƙire su da ƙwaƙwalwar ka, da kuma tunanin ka, 1% ne kawai matsalolin a zahiri gaskiya.
A mafi yawan lokuta, matsalar ba ita ce matsalar ba, yadda kake tunani akan matsalar shi ne matsalar.
Don haka, ya zama lallai ka dakatar da yawaita tunani akan duk wata matsala da kake fuskanta, ka ɗauke ta a matsayin wani abu da ba matsala ba, ka ci-gaba da mu'amala da mutane kamar yadda kake yi a baya, hakan zai rage maka afkawa cikin tunani, rashin yawaita tunani kuma zai rage maka tasirin matsalar ga rayuwar ka, sai ya zamana cewa ma har ta zo ta wuce ba ka ma lura ba.
Kada ka taɓa sarewa kanka gwiwa
Ka daina yin duk wani tunani da ya danganci "Wai shin na cancanci wannan damar kuwa?" A lokacin da wani aiki ya zo kada ka tsaya tunanin ba za ka iya ba, ka shigar da buƙatar ka, komai ta fanjama fanjam.
Kai anya kuwa wannan rubutun zai ƙayatar da mutane? Kada ka yi wannan tunanin, ka wallafa shi kawai. Ko irin "Anya kuwa zan iya" ko kuma "Anya za ta karɓi soyayya ta?" da dai kalolin waɗannan tambayoyin, kada ka taɓa tsayawa irin waɗannan tunane-tunanen, za su dakatar da kai daga yin abinda ya dace, daga baya ka yi da-na-sani, ko yin asarar wata kyakkyawar dama, da ka yi tunanin wani abu mai kyau, ka ƙirga daga ɗaya zuwa biyar kawai ka aiwatar da shi.
Ka dinga tambayar kanka wata muhimmiyar tambaya
A duk lokacin da ka tsinci kanka, kana yawaita tunani akan wata matsala, kuskure, ko masifa da ta faru a baya, sai ka tambayi kanka cewa "shin ko da akwai wani abu da zan yi da zan canza abin da ya faru a baya, ko kuma zai iya taimaka mini wajen inganta gobe na?."
Idan amsar itace eh, to ka ɗauki matakin kiyaye gaba, da yin amfani da shi don inganta goben ka, idan kuma amsar a'a ce, ka bar tunaninsa.
Kodai ka ɗauki mataki, ko ka bar tunani a kai, duk wani abu da ba wannan ba cutar da kai ne!
Tasirin yanzu
Ba za ka iya inganta gobenka ta hanyar yawaita tunani ba!
Ba za ka gyara bayan ka ta hanyar yawaita tunani ba, baya ta riga ta wuce babu abinda zai canza ta.
Duk abin da kake da shi yanzu ne, sannan abinda ka yi yanzu shi ne zai daidaita bayan ka, ya kuma inganta gobenka.
Ka yi bankwana da bayan ka, ka tunkari gobenka, sannan ka riƙe yau ɗin ka, wani mai hikima ya ce "jiya ka girme ta, yau ku ke daidai da ita, gobe kuma ta girme ka". Don haka kada ka taɓa tunanin jiya, ka tunkari gobe ta hanyar yin tunanin abin da za ka yi yau.
Ka dinga tantance tunaninka
Tunaninka zai iya ƙirƙirar maka wasu tsare-tsare da za su bijirar da rashin tsaro a kanka, tsoro da kuma damuwa.
Saboda haka, a kodayaushe yana da matuƙar muhimmanci ka dinga tantance tunaninka kafin ka karɓe su har ma ka tsaya ɓata lokaci kana yin su, "shin ya kamata na tsaya ina irin wannan tunanin?" Daga nan kawai sai ka watsar da su.
Ba don komai ba, sai a lokacin da kake cikin tsananin damuwa, zuciyar ka za ta iya bijiro maka da wasu tunane-tunane marasa tushe bare asali, don haka ya zama lallai ka dinga tantance kalar tunanin da za ka yi, don dai tunaninka dai shi ne kamanni ka!
Karɓar ƙaddara shi ne zaman lafiya
Babu wata damuwa komai yawanta da za ta canza abin da zai faru na gaba a rayuwarka, haka zalika babu wata nadama da za ta canza abin da ya faru a baya.
A kodayaushe ana samun zaman lafiya da kwanciyar hankali a cikin karɓar ƙaddara.
Ka dinga karɓar gyaran da aka yi maka.
Ka dinga karɓar abin da ba ka da tabbas akai duk yadda ya zo maka.
Ka karɓi duk wani abu da ba ka isa sarrafa shi ba.
Ba lallai ka iya fahimtar komai ba, ko jurar komai ba, ko kuma manta komai ba, amma idan har kana son kwanciyar hankali ya zama lallai ka karɓe su a yadda suka zo maka.
Ƙarshe
A ƙarshe dai gaskiyar ita ce mafi yawancin matsaloli ba sa warwarewa da yawaita yin tunani, ana warware su ne da tunani kaɗan.
Za ka samu mafi yawancin amsoshin da kake nema a cikin ƙanƙanin lokaci ba tare da ka ɗauki dogon lokaci kana tunani a kai ba, idan ka fahimci cewa ba za ka iya warware matsalar ba, ka daina gwadawa, sannan ka daina ɓata lokacin ka wajen tunani a kanta, ka yi addu'ar Allah ya kawo mafita, sannan ka mayar da lamarin ga Allah, insha Allah za ka samu cewa matsalar ba ta yi tsamarin da kake tunani ba, fiye da tunanin da ka ɗauki lokaci kana yi a kanta.
Yawan tunani fiye da kima shi ne yake haifar da rashin farin ciki.
Allah ya taimake mu Amin.