1. Farjin mace (vagina) yana cikin ɓagarori na jiki da yake da matuƙar saurin kamuwa da cututtuka, kama daga bacteria, virus zuwa fungi, hakan kuwa ya samu asali ne daga yanayin halittar wannan gaɓa.
Kasancewarsa a buɗe da kuma kasancewar akwai wasu halittu waɗanda ba sa cutar da mace, amma da zarar sun haɗu da wasu ƙwayoyin cuta a waje komai kashinsu sai duk su rikiɗe su dawo ƙwayoyin cuta su fara cutar da ita.
2. Akwai ruwa da mace take fitarwa daga farjinta wanda ba shi da kauri kuma launinsa mai haske ne sannan ba shi da wari kuma babu zafi ko ƙaiƙayi a farjin.
Fitar irin wannan ruwa ba shi da matsala hasali ma hanya ce da jiki yake wanke farjin daga dukkan datti, sai dai daga lokacin da wannan ruwa ya zama yana wari ko ya canza kala zuwa mai duhu ko kuma mace ta lura da akwai ƙaiƙayi ko tana jin zafi musamman ga masu aure lokacin saduwa da mazajensu, to ta garzaya zuwa asibiti ba tare da ɓata lokaci ba.
3. Namiji yana iya sanya wa mace infection ta hanyar saduwa. Wani abun lura kuma shi ne yanayin azzakarin namiji ya sanya shi infection ɗin ba zai nuna da wuri a jikansa ba, haka kuma ba zai fara cutar da shi da wuri ba kamar yadda zai yi wa mace, shiyasa sai ka ga namiji ya sanya wa matarsa infection, shi kuma lafiyarsa ƙalau.
Hakan ba yana nufin namiji ba ya samun infection ba. Shi ma yana samun irin nasa, sai dai ba sosai yake kai na mace tsanani ba.
Za mu tattauna akan infection ɗin namiji nan gaba kaɗan in sha Allah.
4. Abu ne mai tsananin hatsari mace ta ga alamomin infections ba tare da ta yi hanzarin zuwa ganin likita ba. Yana farawa ne daga yanayin rashin hatsari har zuwa lokacin da magance shi yake ƙara wahala.
Shi ya sa ya zama dole mace ta kula da lafiyar farjinta. A shawarce ana so mace ta riƙa zuwa asibitin mata (gynae clinic) aƙalla sau ɗaya a shekara don duba lafiyar farjinta.
5. Tsafta yana da matuƙar muhimmanci wajen lafiyar farjin mace. Ita mace tana iya kamuwa da infection ta hanyar fitsari a waje marasa tsafta. Shi ya sa ake so mata su riƙa kiyayewa daga fitsari a bayan gida da mutane da yawa suke amfani da shi. Idan kuma ya zama dole to ta tabbatar ta samu ruwa ta zuba ko kuma ta yi flushing kafin ta yi fitsarin.
6. A wajen wanka, yana da kyau mace ta riƙa maida hankali wajen ganin cewa ba ta bar sabulu ko kumfa ko wani datti a jikin farjinta ba komai kashinsa, saboda ya kan maƙale sai ƙwayoyin cuta su samu mafaka.
Hakazalika sabulu mai ƙamshi da ke ɗauke da sinadarai daban-daban, amfani da shi wajen wanke farji yana kawo ƙaiƙayi da sauran matsaloli. Sai a kiyaye.
7. Ya zama dole a riƙa kiyayewa wajen yin tsarki. Idan mace ta yi bahaya, ta wanke hannunta tas ba tare da barin sabulu ko kumfa a hannun ba sannan ta fara da wanke farjinta ta kammala shi tas kafin ta wanke bahayan, kar ta kuskura ta taɓa farjinta da hannu bayan ya wanke bahayan saboda akwai ƙwayoyin cuta da za su iya maƙalewa a jikin hannunta, ita kuma mafitsara kamar yadda muka faɗa tana da saurin kamuwa da cuta.
Hakazalika abu ne mai matuƙar hatsari ga mace idan za ta yi tsarkin bahaya ta yi goho ta yadda ruwan wanke bahayan zai iya zuwa ya taɓa mafitsararta. Abin da ya fi dacewa shi ne a nemo toilet paper a fara gogeshi tas, sai a wankeshi ba tare da ruwa ya dawo ya taɓa mafitsara ba.
Iyaye masu 'ya'ya mata, yana da matuƙar muhimmanci ku kiyaye wannan wajen tsaftace 'ya'yanku mata bayan sun yi bahaya.
8. Akwai mata da suke wasa da gabansu ta hanyar sanya yatsa a ciki (fingering da masturbation) wannan ma yana jawo infection ta hanyar ƙwayoyin cuta da suke yatsan mai yin wannan abu. Don haka yana da matuƙar muhimmanci a kiyaye.
9. Ya zama dole a maida hankali wajen kiyaye saka underwear masu riƙe zafi ko kuma masu riƙe zufa da jiƙa ko ruwa, shi ma hakan yana taimaka wa ƙwayoyin cuta su rayu har da hayayyafa a farjin mace.
Tsaftar underwears da kuma tsafta jiki suna da matuƙar muhimmanci. So samu, mace ta riƙa canza panties aƙalla sau uku a rana, sannan idan an wankesu a tabbata an shanya su a rana sun bushe tas!
Hakazalika tsaftar towel da ake goge ciki yana da matuƙar muhimmanci. Yana da kyau a riƙa yawan wanke shi da kuma busar da shi a rana.
10. Idan mace ta lura tana da irin wannan matsala, kamata ya yi ta hanzarta ta garzaya zuwa gun likita, saboda muhimmancin magance wannan ciwo akan lokaci.
Ana yin gwaje-gwaje don gano tsananin da matsalar ta yi da kuma gano maganin da zai kawar da shi ba tare da ɓata lokaci ba. Akan ɗauki sample da ake kira 'vaginal swap' don a yi gwaji a gano wacce iriyar ƙwayar cuta ce ta kama mutum da kuma irin maganin da zai kashe wannan ƙwayar cuta kaitsaye. Ana amfani da magungunan sha da suka haɗa da Anti fungals kamar su fluconazole wadda sha 150mg a lokaci ɗaya kamar yadda WHO ta ba da shawara.
Hakazalika akan ɗaura marasa lafiya akan Doxycycline 100mg bayan kowanne awa 12 (sau biyu kenan a awanni 24) har na tsawon kwana biyar, ana iya ba da Tinidazole ko secnidazole 2g a lokaci ɗaya. Ana kuma bayar da Azithromycin 2g a lokaci ɗaya. Ana kuma iya ba da tablet da ake tura shi a cikin farjin marasa lafiya.
Ana iya sanya shi ta hanyar amfani applicator da za a tura ciki. Akwai cream da ake shafawa ta waje, hakazalika shi ma akwai wanda ake tura shi da applicator ciki. Wannan dai duk bayan an je an ga likita ne kuma an yi gwaje- gwaje. Duk mai neman ƙarin bayanai bayan taje ta ga likita.
11. Irin wannan cuta ya kan haifar da abubuwa da yawa masu muni. Na farko daga ciki shi ne yana tafiyar da ni'imar 'ya mace a wajen saduwa.
Haka zalika wannan cuta ya kan haifar da matsalar rashin haihuwa ga mace idan aka bar shi ya yi tsanani. Wannan dalili ya sa akwai buƙatar ilimantar da mata akan wannan cuta. Don kuwa indai aka kiyaye, kuma aka ɗauki matakin gaggawa da zarar an ga alamunsa to in sha Allahu ba zai kai wannan matsayi ba.
Sai a yi haƙuri yau mun taɓo ɓangaren da yake yi wa mutane da yawa nauyin tattaunawa. Mu dai burinmu al'ummarmu su samu ilimi akan lafiyarsu don magancewa da kiyayewa.
Allah ya ba mu lafiya da zaman lafiya Amin.
Tushe/Asali: Qaloon Health Support