Yana daga cikin abin da ke sanya matasa baƙin ciki shi ne rasa ayyukansu. Kana aiki a ƙarƙashin wani sai a kore ka. Kana aiki a wani kamfani sai a kore ka.
Marubuci:- Khalid A Gombe
Mutum yana yin hidimar kuɗi ne daidai da yadda ake samun su. Yayin da kake aiki kana ɗaukar albashin ₦50,000 to hidimarka da ɗawainiyar ka za su kasance duk cikin wannan kuɗin ne.
To sai kuma aka zo aka kore ka daga aikin ga shi ka saba da hidima ga shi buƙatunka sun yawaita saboda kuɗin da kake samu.
Tabbas abin akwai takaici kuma akwai baƙin ciki matuƙa.
Amma ka san abin da zai sa ka farin ciki?
Idan Allah ya tashi ɗaga darajar mutum sai ya kawo masa sanadi. Kasa a ranka Allah yana son ɗaga darajarka ne shi ya sa ka rasa aikinka domin Allah ya ba ka wanda ya fi wannan.
Mutane da yawa sun zama abin alfahari bayan an kore su daga aiki ne.
Wasu da a ƙarƙashin wani suke amma da aka kore su sun zama suna cin gashin kansu sanadiyyar haka arziki ya samu.
Domin ka samu abin da ya dace da kai wani lokaci sai ka rasa abin da kake so. Kai dai kawai ka yi imani da Allah. Ka sa a ranka cewa hakan sabuwar hanya ce ta yin nasara.