Monday, 9 December 2024

Kafin Ka Fara Kasuwanci Ka Karanta Wannan Sirrin

Tura Wannan Zuwa Ga

Mutane da yawa suna so su fara kasuwanci, amma shawarwari sun yi musu yawa, wasu kuma sun rikice sun ma rasa ta inda za su fara, wasu kuma sun fara amma ba wadda ta dace ba, wasu kuma kansu ya kulle, kawai sun haƙura sun bi yayi.


Kafin Ka Fara Kasuwanci Ka Karanta Wannan Sirrin
Hoto: LinkedIn

Marubuci:- Abubakar Abba


A gefe guda kuma, masana kasuwanci suna ba da shawara cewa kafin ka fara kasuwanci ka yi market research, ma'ana ka yi nazarin kasuwar ka san ma mene mutane suke da buƙata ko kuma mene zai ba ka ribar da kake buƙata.


Da yawa muna so mu yi nazarin kasuwa amma wasunmu ba su san ta ina za su fara ba.


Shi ne ya sa za ka ga mutane da yawa sun kashe kuɗi sun buɗe shago ko sun fara wani kasuwanci amma ba tare da an je ko'ina ba sai ka ga sun rufe saboda ba ciniki, ko kuma ana cinikin amma ba zai iya bayar da ribar da ake buƙata ba, saboda haka, ƙarshe sai dai a kwashe kaya a rufe kasuwanci.


Sau da yawa kai ma kana ganin wasu sun fara kasuwanci a wani wajen za ka ce lallai waɗannan ba su san abin da ya kamata su fara ba, da yawanmu muna ganin irin wannan kusa da mu, kuma muna fahimtar cewa akwai kuskure.


Wani lokacin mutane suna duba abin da yake birge su ne kawai, sai su narka kuɗi su fara kasuwancin wannan abin, ƙarshe kuma su ga mutane sun ƙi ba su haɗin kai.


Wasu kuma, da zarar sun ji an ce abu kaza yana tafiya a kasuwa, sai su yi maza su fara kasuwancinsa, daga ƙarshe kasuwancin ya durƙushe.


Wasu kuma da zarar sun ga wani yana samun kuɗi da wata sana'a, ba tare da sun yi nazarin da ya kamata ba, su ma sai su fara ƙarshe a zo a durƙusar da sana'ar ko kuma bayan sun fara sana'ar su ga ba sa ciniki ko ba sa samun kuɗin da suka yi tsammani za su samu.


Wannan duk yana biyo bayan rashin nazarin kasuwa ne wanda ya kamata.


Ita kasuwa kafin a fara ta akwai buƙatar a yi nazarinta kuma a auna ta.


1. MATSUWA


Abu na farko da ya kamata ka duba kafin ka fara wani kasuwanci a wani waje shi ne, yaya mutanen wajen suke da bukatar wannan abin?


Bayan ka zaɓi irin kasuwancin da kake so ka fara, to ka auna shi a wannan sikelin, idan ka ga mutane suna tsananin buƙatar abin, to lallai kasuwanci ne da za ka iya shiga amma fa bai tsaya iya buƙata ba, akwai wasu ƙarin ma'aunai da za ka duba.


2. GIRMAN KASUWA


Bayan ka duba buƙatar mutane, to abu na gaba shi ne, mutum nawa ne za su iya sayan wannan abin?


Wani lokaci za ka ga tabbas mutane suna buƙatar abin da za ka sayar amma yawan mutanen bai kai ka narka kuɗinka ba.


Idan za ka fara kasuwa to ka tabbata ka yi wannan lissafin.


Misali:


Za ka buɗe shagon cajin waya, sai ka ga duk yankin babu mai caji, kuma ka ga wasu mutanen suna tafiya mai nisa domin su kai cajin wayar su, to ka ga wannan alama ce da ke nuna maka akwai buƙatar shagon caji, to amma sai ka ga ai masu kai cajin su ne kaɗan a mutanen unguwar saboda yawanci suna da solar kuma suna da halin kunna generator, to ka ga anan ba za ka zo ka narka kuɗinka ba, saboda kwastomomin ba za su mayar da abin da za ka kashe ba.


3. FARASHIN DA ZA'A IYA BIYA


Bayan ka yi lissafi, ka ga cewa akwai buƙatar abin da za ka fara, sannan kuma masu buƙatar suna da yawan da za ka samu riba sosai, to abu na gaba shi ne, za su iya biyan farashin da za ka saka?


Wannan yana da matuƙar muhimmanci, duk Ɗan Kasuwar da bai lissafa wannan ba za ku ga ya zo yana ta kumfar baki yana ganin laifin mutane wai sun ƙi daraja sana'ar sa, kuma ba laifinsu ba ne, shi ne bai yi lissafi daidai ba.


Misali:


Idan za ki buɗe wajen gyaran gashi mai daraja, bayan kin gama nazarin kasuwa kin ga buƙatar mutanen wajen, sannan kin ga yawan kwastomomin ki, to sai ki duba; idan kin buɗe irin tsayayyen da kike buri, za su iya biyan kuɗin gyaran gashin da za ki musu?


Kar ki buɗe wajen gyaran gashin 'yan gayu a yankin 'yan koko ba za su zo ba, idan sun zo ma kin faɗa musu farashi, tafiya za su yi su je inda za'ayi musu da arha, domin su ba kwalliya ko adon shagonki ne zai ɗauki hankalin su ba. 


4. SAURIN SAMUN KWASTOMA


Yana da kyau sosai, bayan ka gama wancan nazarin, sai ka duba yaya saurin samun kwastoma yake, kuma nawa za ka kashe kafin samun kwastoma guda ɗaya?


Idan ba ka yi wannan lissafin ba, to zai iya yiwuwa ka zo kana ciniki amma ba ka ganin riba, saboda kuɗin da kake kashewa kafin samun kwastoma yana kusa ko kuma daidai da abin da kwastoma zai ba ka.


Misali:


Wadda ta buɗe shagon gyaran gashi, wajen da ta buɗe mutane ba za su gane ta ba sai ta saka allon talla, sai ta yi ƙatuwar abar talla, sai ta tayar da generator ta kashe kuɗin manfetur sannan za'a san da ita, sannan sai ta yi talla sosai kafin mutane su zo wajen, bayan sun zo kuma, ma'aikata 2 ko 3 ne za su yi musu hidima, kun ga dole su ma a biya su, kuma idan sun zo da farko ba lallai wasu su sake zuwa ba sai an kuma waccar wahalar, to kun ga samun kwastoma 1 ya ci mata kuɗi sosai, to idan ba za ta iya mayar da wancan kuɗin da take kashewa ba akan yawan kwastomomin da za su zo kullum ba, to ba lallai ta gane cewa tana samun riba a cinikin da ake yi a shagon ba.


5. DA ME KA FI SAURA


Idan kana so ka fara wata sana'a ko wani kasuwanci, bayan ka gama nazarinka, yana da kyau ka duba mene ne za ka yi wanda zai bambanta ka da ragowar masu irin wannan sana'ar?


Mafi yawan lokuta mutane ba su cika kallon mene ya kamata su inganta a wani kasuwanci da suke son farawa ba, wanda rashin yin hakan ya sa za ku ga an cunkushe waje ɗaya babu ci gaba, ƙarshe a zo a durƙusar da sana'ar baki ɗayanta.


Akwai ragowar abubuwa 5 wanda ba mu tattauna su anan ba, kuma suna da muhimmanci mutum ya duba su kafin fara wani sabon kasuwanci, ku ci-gaba da bibiyar mu za mu tattauna sosai akan wannan batun da ma ragowar ababen da ba mu tattauna anan ba.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user