Amincin Allah su ƙara tattara su tabbata ga ƙasaitacciyar halittar da kyawunta ya fi na saura, yarda da jinƙan Allah su nake ƙara roƙa miki a kullum da safiya kamar kowacce rana.
Kalaman Kiran Waya Na Barka Da Safiya
Hoto: Dreams time
Marubuci:- Ridwan Khan Adam
Ban da komai ban da kowa sai ƙaunarki don ita ta zama jari kuma aikina.
Ina da tabbacin na fi kowa aikin yi mai kyau a faɗin duniya tun da begen ki da rera miki baitocin ƙauna su zama aikina. Ban da kamarki a rayuwata.