Ji da ganina ya kan gushe a sanadin maraicin rashin sanya ki cikin idanuwana, na kan kasa iya gane wane ne ni a duk lokacin da na tashi daga bacci ban gan ki ba sai na zamo tamkar makaho.
Marubuci:- Ridwan Khan Adam
Son ki a zuciyata dashe ne wanda Allah ya yalwata tamkar shukar da ke samun kulawar ban ruwa a kowacce rana.
Na inganta soyayyarki a cikin zuciya ta domin ke nake yawaita gani cikin baccina da kuma zahirina.
Ke ce wacce idan ban gan ta ba zuciyata ba ta iya jurewa haka kuma idanuwana ba sa iya rintsawa.
Ina ma a ce dukkan nasarar da ke tare da ni a rayuwa ta zamo mallakarki ce, da zan yi alfahari da ke mai sona.
Ki sani cewa zuciyata mai rauni ce ba na iya jure rashin ganin ki cikin idanuwana domin a duk lokacin da na yi rashin ki zan zamo tamkar jaririn da ya rasa gatan sa, ba zan gajiya da ɗawainiyar son ki a zuciyata ba har abada. Daga mai ƙaunar ki har kullum.