Tuesday, 31 December 2024

Kalaman Soyayya Na Asuba

Tura Wannan Zuwa Ga

Ke ce azancin kowanne bigiren hasken da yake ƙara haskaka fadar duniyar masoya, ra'ayina ne kallonki haka zalika ra'ayin kowa ne begenki domin kin cancanta kuma kin dace a daidaita kowanne harafin kalmomi da ambaton kyakkyawar surarki.


Kalaman soyayya na asuba
Hoto: Pinterest

Marubuci:- Yaron MLM KD


Da ke zan shiga taron gudanar da soyayyar gaskiya domin  gabatar da kowanne harafin annurin da yake cikin hasken kyawawan idanuwanki.


Ke ce sarauniyar da nake kishi.


Ke ce tauraruwar cikin ƙalbina.


Ke ce zinariyar da nake tattali da kulawa.


Ke ce kyakkyawar da nake alfahari da ita.


Ke ce autar da ke cikin fadar zuciyata.


Ke ce sinadarin hasken idanuwana.


Sha bege da kirari a cikin kalamaina.


Ke ce kowanne nau'in farin cikina.


Ke ce ma'abociyar kowanne murmushina.


Ke kika zamo jigon nishaɗina a soyayya.


Da ke zan kasance a kowane yanayi.


Farkon kallon da na yi miki shi ne cikakken bayanin shigowarki a cikin ƙalbina. Asalin kyawunki gami da haskenki shi ne lantarkin kyakkyawar kwalliyar da take bayyana annurin idanuwanki.


Tsarin sautin amon tattausar muryarki ya zarce ayarin kalmomin lafazin da zan iya furtawa ma'abocin sauraro, diri da haibarki su ne misalin kamannin kyakkyawar Gimbiyar da za'a kirata Sarauniyar masarautar birni da karkara.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user