Ruƙayya Ahmad Aliyu wadda aka fi sani da Rukky Alim ɗaya ce daga cikin sababbin jarumai mata masu tasowa a masana'antar Kannywood.
Hotunan sun ɗauki hankula sosai a shafukan Sada Zumunta duba da yanayin yadda aka ɗauki hotunan, wanda hakan ya taka muhimmiyar rawa sosai wajen ƙayatar da al'umma daga sassa daban-daban na faɗin duniya.
Rukky Alim ɗaya ce daga cikin jaruman da ke jan ragamar shiri mai dogon zango a halin yanzu mai suna Allura Cikin Ruwa.
Waɗannan wasu ne daga cikin kyawawan hotunan nata.
Ƙalli ƙarin wasu hotunan a ƙasa:
Ku ci-gaba da kasancewa tare da mu a kodayaushe domin samun ainihin cikakken tarihin Rukky Alim nan ba da jimawa ba tare da zafafan hotunan ta na musamman.