Idan ɗayanku ya auri mace, ko ya sayi bawa mai hidima, sai ya ce;
اَللَّهُمَّ إِنِّي أَسْأَلُكَ خَيْرَهَا، وَخَيْرَ مَا جَبَلْتَهَا عَلَيْهِ، وَأَعُوذُ بِكَ مِنْ شَرِّهَا، وَشَرِّ مَا جَبَلْتَهَا عَلَيْهِ.
Allahumma innee as-aluka khayraha wakhayra ma jabaltaha 'alayh, wa-a'oothu bika min sharriha washarri ma jabaltaha 'alayh.
Addu'ar Wanda Ya Yi Sabon Aure Ko Ya Sayi Abin Hawa
Hoto: Seekers guidance
Ya Allah ina roƙon Ka alherin ta da alherin da Ka ɗabi'antar da ita a kansa, kuma ina neman tsarinka daga sharrinta da sharrin da ka ɗabi'antar da ita a kansa.
Idan kuma ya sayi raƙumi, to ya kama tozon raƙumin ya faɗi kwatankwacin wannan (addu'ar).