Ƙasidar Duniya Budurwar Wawa Ta Sa'eed Ibrahim
Hoto: Rollover/iStock photo
Zuciya tana mini rauni, ta hana ni in yi sukuni, watarana za mu rabu dukan mu ba za mu sake gamo ba.
Lamarin yana mini tsauri, a cikin bugawar fari, babu wanda sam ya sani idan ba kaliƙin mu guda ba.
A cikin watan watarana za a yanke duk wata ƙauna, dukkanin abin da ka mallaka ba za a kai ka da shi ba.
Daɗa yanzu ka zama gawa, haka za a kai ka kushewa, daga kai kaɗai sai ayyukan da ka aikata ba wai ba.
Duniyar ga ƙyalƙyal banza, kyan macijiya ba izza, walwali take daga nesa in ka iso ba za ka gani ba.
Yaudarar tana mini zafi, da shigo-shigo ba zurfi, ran da duk ka bi ta ta kai ka inda ba za ka ko dawo ba.
Shi agogo ba ya baya, kuma lokaci bai ƙarya, duk irin da kai ka dasa shi dole akwai yinin yin girba.
Furfura alamar tsufa, yau da gobe tamkar jifa, lokacin ka ba ya jira idan ya wuce ba zai dawo ba.
Ga jikin ka ba shi da ƙwari, yara duniya labari, duk abin da za ka saye shi don ka ci sam ba zai daɗi ba.
Maigidan ka ya mutu shi ma, mutuwar ka ba ta girma, jinjiri ya kan mutu saurayi yai rayuwa gwaggwaɓa.
Ka taho kana yin kuka, ka mace ana maka kuka, da bazar ka ne wasu ke rawa ba su so a ce ka kau ba.
Wasu sun mace sun huta, wasu sun wuce an huta, kar ka zam a gundura har da za ka mace ba ai kewa ba.
Ka yi tarbiyyar 'ya'yan ka in ka tsufa za su ji ƙan ka, haka nan idan ka mace ba za su gushe suna addu'a ba.
Annabin ka ne baƙon ka, girmama shi kar ka guje shi kar ya guje ka, wanda duk ya girmama Ɗan Adam ba zai rashin matsayi ba.
Arzikin ka na a jikin ka, zai biyo ka kan ajalin ka, bi a hankali dukkan rabon ka ba za ya zo ya wuce ba.
Duniya gidan kashe ahu, la'ila ha illallahu, yanzu ƙila likkafanin ka ya isa kasuwa ba ka sani ba.
Sa'eed Ibrahim ne wanda ya gabatar da wannan ƙasida mai cike da saƙonni masu amfanarwa ga kowa, wakilin mu kuma ya fitar muku da baitocin ƙasidar a rubuce domin ilimantarwa da fadakarwa a gare mu gabaɗaya.
Ku ci-gaba da kasancewa tare da mu a kullum don ci gaba da samun zafafan ƙasidu a rubuce masu ma'ana tare da waƙoƙi a rubuce su ma masu ma'ana.