Safiya mafarin dukkan wuni. Ina fatan kin wayi gari lafiya tsokar jikina, duk da na san mun zanta kafin hakan, amma abun ka da mai ƙaunar ka sai ya ƙara jaddada hakan idan zuciyar ta motsa, Zainab ina ƙaunar ki ƙauna mai cike da girmamawa da kulawa.
Marubuci:- Yaron MLM KD
Ba na tunawa da ko ranar haihuwata ko kuma ranar kammala karatuna domin har yanzu da sauran na yi farin ciki, ranar bikin mu ita ce ranar haifata kuma ita ce ranar kammala ɗan ilimin da nake nema. Allah ya faranta miki ƙanwata koda ni na gaza.
Karramawa da aminci, gami da kuma tausayawa nake miki. Ina fatan hakan ya ɗore har zuwa lokacin da za mu koma ga mahaliccin mu mu yi rayuwar 'yanci, sahibata wallahi ƙaunar da nake miki sunan ta ya fi ƙarfin na kira ta da so sai dai na ce mata kankat.
Ranar auren ki ta zama kamar ranar samun 'yanci ce gare ni. Ina ƙaunar ki matuƙa mu wuni lafiya. Bissalam.
Daga naku Sarkin Masoya. Ku ci-gaba da kasancewa tare da ni a kullum a wannan shafin.