1. Maƙiya su ne abokan bogin da ka sani, abokan bogi su ne maƙiyan da ba ka sani ba.
2. Maƙiya za su maka fatan mutuwa, abokan bogi za su haƙa ramin binne ka.
3. Maƙiya su ne sheɗanun da ka ke gudu, abokan bogi su ne sheɗanun da za ku mutu tare.
Maƙiyi da Abokin Bogi da Abokin Gaskiya
Hoto: We are brothers
Marubuci: Anas Darazo
4. Maƙiya su ne ka ke yi wa fatan kada su yi nasara, abokan bogi ke fatan kada kai nasara.
5. Maƙiya su ne su ke fatan kai ka ƙasa, abokan bogi su ne masu kai ka ƙasa.
6. Ko ka san za ka iya sanin maƙiyi zai kawo maka hari, amma abokin bogi shi ke ma ka yankan baya.
7. Zagin maƙiyi ya fi alheri akan shawarar abokin bogi.
8. Shugaban su gabaɗaya, shi ne aboki na gaskiya; maƙiyi zai iya harbin ka, abogin bogi zai maka yankan baya, abokin gaske zai mutu a kanka.
9. Abokin bogi zai yayata laifukan ka, abokin gaskiya zai gyara maka su.
10. Abokin bogi zai rungume ka ya ce jikinka yana wari, abokin gaskiya zai saya maka turare bayan ya rungume ka.
11. Abokin bogi zai taya ka ku cinye kuɗin ka ya ci zarafin ka bayan ka talauce, abokin gaskiya zai saka ka juya kuɗaɗen ka ya ba ka goyon baya idan ka talauce.
12. Abokan bogi za su yayata sirrinka, abokan gaske za su ɓoye sirrinka.
Mcedopikin ne ya faɗa a bidiyon sa, ni kuma na rubuta na fassara.