Akwai ƙananun abubuwa da suke sa namiji ya ji yana bala'in son mace wallahi, amma matan Hausawa ba su ankare da su ba kuma sam ba su ba su muhimmanci ba, su kawai burinsu a yi ta zuba kalaman soyayya kuma namiji ya yi ta musu hidima kamar sun siyo bawa a kasuwa.
Marubuci:- Abdallah Aliyu Saint
Akwai abubuwa da yawa wanda za ki ja hankalin namiji wanda wallahi mai raba ku sai rabbul samawa wati ina magana akan 'yammata ne ba masu aure ba.
Yi masa 'yar kyauta kamar saya masa maɓalli hannun riga (Links), ɗan turare, 'yar hula mara tsada, ɗan silifas ko na shiga wanka ne, na taɓa wata budurwa da take saya min irin waɗannan abubuwan duk da na san cewa hidimar da nake mata ta fi abin da take min wallahi duk abin da ta saya mini sai na ji na fi sonsa akan wanda na saya da kuɗina koda kuwa ya fi nata tsada.
Mun sani cewa mata mugayen marowata ne shi ya sa namiji yake tabbatarwa duk macen da ya ci kuɗinta koda kaɗan ne to ya tabbatar tana son sa da gaske ba wasa ba.
Amma matan Hausawa ba su cika wannan ba sai wadda wayewarta ta kai, su burinsu su yi ta karɓar naka kamar tsofaffun almajirai, ko kuma sun yi ƙoƙari su girka maka wata bushashshiyar dafaduka (Jallop) ko mai bai ishe ta ba da wani lemo ɗan haɗi, kuma wasunsu da wata manufa suke yi.
Idan kina da hali wani lokacin ki turawa saurayinki kati ko data shi ma fa mutum ne akwai lokacin da yake buƙatar su kuma wallahi ba shi da ko sisi haka zai ji son ki ya ƙara ƙaruwa a ransa.