Monday, 9 December 2024

Sahihiyar Hanyar Cikar Kowanne Buri A Rayuwa

Tura Wannan Zuwa Ga

Da farko dai a duk inda muka nufa abu na farko muna da buƙatar sanin kaitsaye ina muka nufa? Don haka sai mu san wacce hanya za mu bi, sannan wanne kalar hanyar sufuri za mu yi amfani da shi mota ko jirgi da sauran su to haka ma idan muna so mu cimma wani abu, abu na farko ya zama dole mu gano mene ne burin mu? Idan ba mu yi wannan ba, duk wani mataki da za mu bi ba zai yi mana aiki ba yadda ya kamata, zai iya yiwuwa mu bi wata hanya can da ba za ta ɓille da mu ba, ko hanya mai sarƙaƙiya, kai a taƙaice ma yanzu kai ne za ka yi tafiya ba ka san inda za ka ba, shin wanne hali za ka shiga? To haka wanda ya ke tafiya a rayuwar sa babu wata manufa babu wani buri to shi wannan ya zama cikakken wahalalle mara alƙibla.


Sahihiyar Hanyar Cikar Kowanne Buri A Rayuwa
Hoto: Dallin cooper

Marubuci:- Ibraheem Aleeyu


To, a wannan rubutun zan yi iya bakin ƙoƙarina wajen gabatar muku da SMART RULE, wato wasu ƙa'idoji da mutum zai yi amfani da su wajen tsara manufofin rayuwar sa ta hanyar da ta dace, kuma da zai samu sauƙin kai wa ga inda ya dosa.


Waɗannan ƙa'idoji na SMART RULE an yi bayanin su a manyan littattafai cikin wadataccen bayani kuma daki-daki, misali littafin Goal setting 101 na Gary Ryan,  da kuma The power of Goal setting na Rohn, da kuma babban littafin nan da ya shahara wato Goals: How to get everything you want faster than you ever thought possible na shahararren marubuci Brian Tracy, duka a cikin waɗannan littafai ba wai iya ƙa'idar SMART RULE aka yi bayani akai ba, da akwai wasu ƙarin shawarwari da za su ba ka damar tsara manufofin ka, ta yadda za ka kai ga cimmu su cikin sauƙi, amma ni dai yanzu zan yi taƙaitaccen bayani ne gwargwadon fahimta ta game da SMART RULE, biyo ni.


Ana yawan cewa tsararriyar manufa, da aka gina bisa kyakkyawan tsari rabin yaƙi ne, a gabatarwar littafin The richest man in babylon marubucin ya ce kada ka yi komai sai ka yi nazari da tunani a kansa, haka zalika kada ka yi nazari akan komai sai ka san shi, bisa ga haka SMART RULE ƙunshi ne na wasu kalmomi wato burinka sai ya zama Tantancewa, Aunawa, Cimma buri, Dacewa, sannan kuma Ƙayyade lokaci.


Ga su kamar haka:


Tantancewa


Na nufin dole ya kasance ka tsaya ka tantance, ka gane asalin abin da kake son ka cimma. Wannan bayani ne da na yi tun a baya, kamar yadda ba zai yiwu ko zai yi matuƙar ba ka wahala fara tafiyar da ba ka san inda za ka ba, to haka nan ba zai yiwu ka cika wata manufa da ba ma ka riga ka tsara ta ba, shin ko zai yiwu?


Misali


Ko, ina son na zama marubuci, to me za ka rubuta,(ba a tantance shi ba), amma idan ka ce ina son na rubuta shafi biyu kullum (an tantance shi).


Ko, ina son na yi kuɗi, wannan ba a tantance shi ba.


Ko game da kasuwanci ka ce ina son samun riba kullum (ba a tantance shi ba) amma ina son samun ribar ₦2,000 kullum (An tantance shi).


Ko ina son na dinga samun ƙarin masu sayan kayana kullum (ba a tantance shi ba), ina son ƙarin masu siyan kayana kullum da kaso ashirin cikin ɗari (An tantance shi).


Aunawa


Wannan kaitsaye zai ba ka amsar tambaya ne ta ya zan san na yi nasara? Dole ya kasance da akwai wani ma'auni da za ka iya auna nasarar ka.


Misali


Ka ce ina son na samu ƙarin mabiya a wannan watan (ba a auna ba), amma idan ka ce ina son ƙarin samun mabiya da kaso ashirin cikin ɗari a sati, wannan kuma an auna shi.


Auna muradi kamar allon kafe makin ka ne, zai taimaka wajen gane ci-gaban da kake samu, da lokacin da ka ci nasara.


Cimma buri


Dole ya kasance za ka iya cimma wannan burin, gwargwadon abin da kake da shi na dabaru, kayan aiki, jari, halin da kake ciki da sauran su.


Misali


Ka ce ina son na samu ƙarin mabiya miliyan ɗaya (muradin da ba a iya cimma).


Ko ina son na koyi yaren programming na Python, ko gina shafin yanar gizo, ko shafin smart contact na blockchain a kwana ɗaya (wanda ba za a iya cimma ba), amma a shekara ɗaya, biyu ko uku. Wannan shi ne wanda za'a iya cimma.


Dacewa


Ya zama ya dangance ka, cimma shi zai yi matuƙar tasiri wajen canza rayuwarka, ko sana'arka ma'ana yana tafiya ne da ɗaga darajarka daga yadda kake yanzu zuwa sama da haka.


Misali


Ba ka taɓa jin kana son waƙa ba amma ka ce kana son ka ƙware a kaɗa garaya ko jita, ko ba ruwanka da kwalliya a matsayin namiji amma ka ce kana son koya, da sauran su amma ya zama kana son zama engineer to ka karanci engineering, kana son zama web developer ka koyi HTML, c,s,s, javascript, Php, Node.js, MySQL da sauransu.


Wannan shi ne zai nuna maka kaitsaye inda ya kamata ka bi domin cimma manufofin ka.


Ƙayyade lokaci


Dole ya zama da akwai lokacin da ka tsara za ka cimma wannan manufar kafin ya wuce, jadawalin aiki da lokacin da za ka gama kowanne mataki,  da sauransu.


Misali


Ka ce ina son na koyi web development watarana (lokacin da ba a ƙayyade ba) amma ina son na koyi web dev nan da shekara ɗaya, (lokacin da aka ƙayyade), ko ina son rubuta littafi (lokacin da ba a ƙayyade shi ba), sai dai nan da ƙarshen wannan shekarar zan yi kaza. Lokacin da aka ƙayyade.


Waɗannan su ne suka haɗa harufan SMART RULE wanda zai yi wa kowa sauƙin haddacewa, haka zalika idan kana da wani babban buri, za ka iya raba shi mataik-mataki, idan ka gama da wannan sai ka haura na gaba.


Fatan ka amfana da wannan rubutu, yaɗa wannan rubutun ga abokan ka na musamman.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user