Da yawan masoya na rabuwa saboda tilastawa daga wajen mahaifan ɗaya daga cikinsu, idan irin hakan ta faru gare ka, ga kaɗan daga irin saƙon da za ka tura mata domin jawo hankalin yarinyar gare ka.
Marubuci: Imran Musa Jahun
Ga su kamar haka:
Me ya sa ake son na rasa rayuwata tunda sauran ƙuruciyata?
Ban taɓa ganin inda aka raba hanta da jini ba kuma aka rayu ba.
Babu sauran numfashi daga ranar da zuciya ta daina amsar jini.
Babu sauran farin ciki daga ranar da aka raba uwa da ɗan ta.
Rayuwa za ta zamo mai ƙunci gare ni daga ranar da aka raba ni da ke.
Me ya sa ake son rusa tanadin da na daɗe ina yi miki don kyautata rayuwarki?
Zan iya jurewa duk ƙaddara amma ban da ta rasa ki, har yanzu ina kallonki a matsayin matata.
Har gobe zuciyata tana muradinki, kuma rayuwata ta ginu saman farin ciki saboda tarayyar soyayyar mu, yanzu aka raba mu mece ce makomar rayuwar mu?