Monday, 2 December 2024

Sakonnin Soyayya Na Bayyana Damuwar Zuciya Ga Budurwa

Tura Wannan Zuwa Ga

Ba ni da laifi domin ko shawara zuciyata ba ta nema ba a lokacin da sonki ya kawo ziyarar bazata, sai dai kawai na ji farin cikina,burina,walwala da annashuwata duk suna a cikin duban tsaleleiyar fuskarki ne.


Saƙonnin Soyayya Na Bayyana Damuwar Zuciya Ga Budurwa
Hoto: Mirror

MarubuciImran Musa Jahun


Yanzu na yi laifi idan na nemarwa raina abinda ya fi so? Koda ba za ki so ni ba, to ina alfahari da cewa ba za ki taɓa samun wanda ƙaunarki ta cuɗanya da farin cikinsa ba tamkar ni.


Ban da laifi, ki yi tunani za ki tabbatar da hakan domin burin zuciya samun abin da take so. Don haka ya zama dole na sanar da ke cewa ke ce zuciyata ke so.


Ni kaina ban san lokacin da zuciyata ta kamu da tsananin ƙaunarki ba.


Sau da yawa na kan rasa bacci saboda tsananin zafin son ki, na daɗe ina zama dirshan a hanyoyin wucewarki domin kawai na ga tafiyarki irin ta ƙasaita. Ke ce kaɗai ke wahaltar da tunanina, ki yi mini uzuri.


A ƙarshe ina fatan kalamaina za su zamo masu sauƙin fahimta a gare ki.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user