Taswirar gurbin kasuwa ya fi tsarin sanin ƙarfin sana’a, da gazawa, da damarmaki da barazana wahalar fahimta dangane da gano matsayin sana’ar ka idan ka kwatanta da masu gasa da kai. Taswirar gurbin kasuwa zane ne wanda yake nuna kasuwa da hajar da take gabatarwa, ta yadda ido zai iya gani domin fahimtar kishiyoyi.
Marubuci: Bello Galadanchi
Wannan tsari yana da amfani sosai domin fahimtar da sana’a yadda za ta nuna wa jama’a irin tsarin sana’ar mutum da abin da yake gabatar wa, idan aka kwatanta da masu gasa da ita.
Domin fahimtar taswirar gurbin kasuwa, mai ƙoƙarin fara sana’a zai yi ƙoƙarin sanin abubuwa kamar uku zuwa biyar da ke saka kwastoma yake amincewa ya ɗauki kuɗinsa ya bayar, musamman idan ya kwatanta da waɗanda ke gasa da shi.
Bari na baku misali, idan ka ɗauki fasaha, kayan ado, ko ƙwarancewa wajen gabatar da abu, ko nishaɗi. Wasu abubuwa da za’a a iya dubawa su ne farashi (da tsada ko sauƙi, tsarin mutanen jiya ne ko na wannan zamani, akwai inganci ko babu??) Waɗannan tsarurruka guda uku da ke zumunci ko gasa da juna, za’a iya tattaro bayanai da za’a iya ƙirgawa domin fahimtar yadda kwastomomi suke kallon sana’a.
Abun da manajoji suka fahimta daga binciken da manazarta suka yi shi ne, za’a iya saka duka hajojin da ake gabatar wa a kasuwa akan taswira ɗaya.
Za’a iya rubuta adadin haja da kwastoma ke so a ɓangare daban-daban a taswira ɗaya, sau da yawa, abin da manazarta suke yi shi ne ƙiyasta wannan zane da kuma yin watsi da adadin gurbin kasuwa.
A ƙarshe sana’a za ta iya nazarin yin shinkafa da wake da taswirorin gurbin kasuwa, da za su bayyana abubuwa daban-daban, da kuma yin nazarin su domin bai wa sana’a idon fahimtar matsayinta a kasuwa.
Wanda idon sa yake a buɗe, shi ne ya san hanya cikin sauƙi.