Thursday, 5 December 2024

Tafiya Kai Kadai Don Cimma Buri

Tura Wannan Zuwa Ga

Mutane da yawa za ku tafi tare amma suna iya barin ka a kodayaushe, ka koyi tafiyar kai kaɗai saboda babu wanda zai tabbata a tare da kai. Kada ka ji tsoron tafiya akan hanyar nasara koda hakan na nufin za ka tafi kai kaɗai ne.


Tafiya Kai Kaɗai Don Cimma Buri
Hoto: Tongsai/Shutterstock

Marubuci:- Khalid A Gombe


A hanyarka ta kai wa zuwa garin nasara ba lallai ka samu abokan tafiya ba, ba lallai ka samu guzuri ba, sannan ba lallai ka samu jagora ba.


Kada ka ji tsoro don kana tafiya zuwa ga nasara kai kaɗai, da ma haka nasara take wani lokaci kai kaɗai kake hangen ta da zarar ka same ta sai ka ga kowa ya gan ta a tare da kai.


Kada ka ji tsoro don tunaninka ya bambanta da na sauran mutane da kake rayuwa da su. Kada ka ji tsoro don ra'ayinka ya bambanta da na saura. Kai dai ka tabbatar ka yi tunani mai kyau sannan ka tabbatar ra'ayinka mai kyau ne.


Ka fara yarda da kanka koda mutane ba za su yarda da kai ba. Wani lokacin hasken rana yana fitowa sai hadari ya zo ya kare sai mutane su ga duhu, duk da suna ganin duhun amma hakan ba ya nufin babu hasken rana. To haka gaskiya da amana take wani lokacin kai kaɗai ka san ta, kai kaɗai ka yi imani da ita kafin ta bayyana a idon kowa.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user