Monday, 2 December 2024

Taswirar Kasuwa Mai Kawo Riba

Tura Wannan Zuwa Ga

Dalilin bincike da fahimtar taswirar kasuwa shi ne gano damarmaki ta inda mai son fara sana’a zai iya bambanta kansa daga masu gasa da shi. Waɗannan damarmakin za su bai wa sana’ar daraja irin nata, kuma za’a iya tallata wannan daraja domin buɗe idanun kwastomomi da jawo hankalin su saboda an kawo musu sabon abu mai amfani kuma babu irin shi a kasuwa. Wannan taswira kuma za ta bayyana ɓangaren kasuwa da aka fi yawa, wato sana’ar da kowa yake yi, ko darajar da kowa yake gabatarwa.


Taswirar Kasuwa Mai Kawo Riba
Hoto: LinkedIn

MarubuciBello Galadanchi


Idan za ka fara sabuwar sana’a, to taswirar kasuwa zai iya nuna maka gurbin kasuwa, gurbi mai kyau ta inda za ka fi mayar da hankali akan sana’ar ka a yayin da kake fama da ƙalubalen shiga cikin kasuwa. 


Sana’a’o’i da kamfanonin da suka riga suka kafu, za su iya amfani da taswirar kasuwa tare da nazarin KGDB (ƘARFI-GAZAWA-DAMA-BARAZANA) domin binciko sababbin damarmaki da kuma yanke shawara akan ko sana’ar na da ƙarfin shiga wani gurbin kasuwa. 


Taswirar kasuwa na taimakawa wajen sanar da mai sana’a akan dabarun da zai iya yi wajen gabatar da haja tare da gujewa masu gasa yadda sana’ar za ta fi daraja. 


Binciken kasuwa domin gano gurbi shi ne dalilin kafuwar shagon shayin TWG a Singapo a lokacin da aka gano cewa babu shagon shayi na masu kuɗi kuma dattawa, inda za su share lokaci mai tsawo suna ‘yan karance-karance, da hutawa da shaƙatawa, ba irin waje na samari ba kamar Starbucks inda shayin ya fi sauƙi, amma tsarin wajen da hayaniyar yara da samari ba zai ƙyale dattawa su sake ba. 


An buɗe TWG a shekara ta 2008, ga shi yanzu yana da shaguna da dama a duk faɗin duniya. Wannan babban misali ne na gano gurbin kasuwa irin wanda babu kamar shi, da kuma samar da haja da tsari da ya bai wa sana’ar ma’ana da daraja ga waɗanda suke buƙata.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user