Hmm Allahu ga bawanka nan.
Kewa nake in ba ya nan.
Kare shi Allah ko'ina yake ka sa ya tuna da ni.
Kula da shi namijin gari.
Ya fi min maza miliyan ɗari.
Na ƙuna ba na jin bari a kansa ku mini uziri.
Hm ƙauna da son ki nake zara.
To kin ga dole na yunƙura.
In babu ke wa zan hara?
Rashin ki zai shiga makara.
Dubun maza ba su kai ni ba.
Don ba su samu kamar ki ba.
Baki ka gan shi yana zuba sai in ƙi na kusa daf da ni.
Ka iya soyayya, ita 'ya mace ka ga tana son rarrashi.
Da nuna kulawar nan ka ji ƙauna wacce ake yi wa alwashi.
Ka zarce maza iya kallon so mai sanya gaɓa ta jiki laushi.
In ka bar ni cikin su maza ban san kuma wa zan ɗauko ba?
Bari!! Wannan batu bai min daɗi ba a kunnena.
In na bar ki na bar baya da ƙura, ya za nai da magautana?
Ke na gasgata ke zan kai gidanmu, ki gai da iyayena, tamkar jariri haka za ki yo ɗawainiya gun rainona.
Na ƙi!! Ni ba za a kai ni ba.
Ina ne wai ba za a je a kai ki ba?
Gidan wanin ka ba zan je shi ba.
Ni ma ba zan bari a raba mu ba.
Ka waiwayo kallon ka bai ishe ni ba.
Har abada ba za na daina son ki ba.
Da kai na so zama ba zan bar ka ba.
Kowa ya kula ki ban yafe shi ba.
Mawaƙi Bash A. Adam tare da mawaƙiya Fati Khalil Zabia ne su rera wannan waƙar, wakilin mu kuma ya fitar muku da baitocin ta a rubuce don jin daɗi ku. Musamman masoya da ma'aurata.
Ku ci-gaba da kasancewa tare da mu a kullum don ci gaba da samun zafafan waƙoƙi a rubuce da ƙasidu a rubuce.