Daga shekaru 20, zuwa 25, idan Allah ya ba ka aron dama kada ka yi wasa da ita, ka maida hankali ka amfane ta a inda ya dace domin wannan shi ne lokaci mafi hatsari ga rayuwar ka, saboda a cikin sa ne dai kake da zaɓi guda biyu; kodai ka gina ko kuma ka rusa rayuwar ka.
Marubuci:- Abdulfatah Yakubu
Idan karatu za ka yi, kafin ka rufe shekaru 25 za ka iya gama Secondary school, NCE, ND, HND, har zuwa matakin Degree, ya danganta da yanayi da kuma yankin da ka taso.
Ba iya karatun boko ba, hatta ɓangaren karatun addini idan ka maida hankali a wannan shekaru biyar za ka sha mamakin ilimin da za ka tara.
Idan kasuwanci, ko sana'a za ka yi, to wannan shi ne lokacin da ya fi dacewa ka fara, aƙalla kana da shekaru biyar wanda indai ka maida hankali to ba makawa za ka samu ƙwarewa ta ban mamaki, sannan duk wani ɓoyayyen sirri da yake ƙunshe a cikin wannan sana'ar za ka same shi daidai gwargwado, dadin daɗawa kuma za ka koyi mu'amula da mutane da yawa kama daga masu irin sana'ar ka da kuma abokan cinikayya (customers) wanda hakan zai bayu izuwa ƙulla alaƙa mai dogon zango (connection).
Ba iya karatu ko sana'a ba, duk wani lissafi ana yin sa ne kafin akai shekaru 25, dalili kuwa shi ne; a wannan lokacin ne kake kan ganiyar ka, ga yalwar lokaci, lafiya da kuma cikakkiyar natsuwa (ta zahiri), babu mamaki ma wannan lokacin a gida ake ɗaukar nauyin ka, ka ga kam komai daidai ne ba kada wata matsala.
Kada ka damu akan dole sai komai ya tafi daidai, da ma shekaru ne na koyo da gwadawa, kai dai ka ci gaba da jarabawa, domin a wannan lokacin koda kuskure ka yi, zai fi maka sauƙin gyarawa saɓanin a ce shekaru sun fara cimma ka.
Wannan 'yar taƙaitacciyar nasiha ce zuwa ga iyaye, da su kansu ƙannen mu musamman ma waɗanda suke tsakanin shekaru 20 zuwa 25. Dan Allah dan annabi ku maida hankali wajen gina rayuwar ku.
Da ni da kai kuma da muka haura waɗannan shekaru, har yanzu dai ba mu makara ba, za mu iya natsuwa mu gyara inda muke da kurakurai, domin masu hikima suna cewa "Ba ka makara ba, har sai ka ji ka a makara."
Rayuwa za ta maka duk uzurin da ya kamata ta maka, amma kana haura shekaru 25 za ta juya maka baya.
Ka lissafa duk abin da kake son lissafawa tun yanzu domin nan gaba ba kowacce kalar kalkuleta (Culculator) ce za ta maka aiki ba.