Friday, 20 December 2024

Wasikar Fatan Alkhairi Tare Da Neman Afuwar Masoyiya

Tura Wannan Zuwa Ga

ZUWA GA KYAKKYAWAR MASOYIYATA



Ina yi miki fatan alkhairi, mafi daraja daga  kowanne da na taɓa yi miki a tsawon tarayyar soyayyar mu. Na turo wannan ne don neman afuwar laifina wanda dalilin sa ne idanuwana ke jin kunyar kallon ƙasaitacciyar fuskarki.


Wasikar Fatan Alkhairi Tare Da Neman Afuwar Masoyiya
Hoto: Freepik

MarubuciAbba Rabi'u Matallawa

Ina sanar da ke cewa ban janye daga gare ki don tsoro ko ƙiyayya ko waninsu ba.


Ran ki ya daɗe ki tuna fa ke ce mace ɗaya tilo, haka kuma macen farko da ta mallaki soyayyata ta gaskiya.


Sannan kuma macen da nake kwana da wuni da tunaninta, ashe kuwa ba zai yiwu na guje ki don ƙiyayya ba. Ke ce zaɓin zuciya a jiya da yau da gobe.


Fatana shi ne ki amshi uzurina a lokachin da kika kammala karanta saƙona. Ki kasance lafiya.


Daga naki Abba Rabi'u Matallawa.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user