Ka yi babban tunani, sannan ka fara aiki a hankali don cimma wannan tunanin naka. Ka yi tunanin zama kamar ɗangote, ko samar da wani babban kasuwanci, ko??
Marubuci:- Ibraheem Aleeyu
Abubuwa da dama da kake tunanin cimma su zai iya zama ƙololuwar cin nasara a wurin ka, hasashen wasu abubuwa masu muhimmanci da kuma gina kyakkyawar rayuwa a nan gaba.
Kalar wannan tunanin zai taimaka maka wajen ƙara maka karsashi, faɗaɗa tunaninka, da kuma jawo ci-gaba ga rayuwa sakamakon samarwa da kai wata manufa da ake son a cimma.
Bayan wannan tunanin sai kuma fara aiki, ya zama lallai ka fara yin wani abu da zai kai ka ga cimma manufarka, wata kila Ɗan Kasuwa kake son zama to ka fara sana'a, sannan ba sai ka jira samun babban jari ba za ka fara, kawai ka fara yau, don kuwa ba ka buƙatar zama shahararre don ka fara amma kana buƙatar farawa don zama shahararre, ka bi komai a hankali kuma daki-daki har ka cika manufarka, ba zai yiwu ka cika wannan burin naka a dare guda ko lokaci guda ba. Don haka sai ka yi aiki da kaɗan da kaɗan har ka cimma manufofin ka.