Monday, 16 December 2024

Yadda Faduwa Za Ta Sauya Rayuwar Ku Nan Take

Tura Wannan Zuwa Ga

Mutane da yawa kan yi baƙin ciki ko sarewa daga abin da suka sanya a gaba sakamakon rashin nasara, wannan shi ne babban kuskuren  da za ka yi a rayuwa wai dalilin rashin nasara ka dakatar da sana'a, karatu, da sauran su kuma ina mai tabbatar maka da cewa za ka yi da-na-sani watarana matuƙar ka sare.


Yadda Faduwa Za Ta Sauya Rayuwar Ku Nan Take
Hoto: LinkedIn

Marubuci:- Ibraheem Aleeyu


Misali 


wasu ne a shekarar Bara waccan su ka tashi daga garin mu tare da yin tafiya mai nisa har jihar Taraba su ka yi noman  shinkafa, wanda ake sa ran samun riba mai yawa, amma bisa ƙaddara sai aka yi ambaliya kuma noman ya lalace, hakan ya sa shekarar da ta gabata aka ce ko za su yi? Sai suka ce "A'a", ma'ana dai suna jin tsoron sake yin rashin nasara kamar shekarar da ta gabata, amma kuma cikin ikon Allah wannan shekarar sai aka samu alheri mai yawa, kuma na ji da yawa daga cikinsu suna cewa da sun sani sun yi noman a wannan shekarar. Wannan zai iya zama sakamakon duk wani wanda ya yi rashin nasara har hakan ya zama dalili na sarewarsa wato nadama a ƙarshe.


Wani ɗan jaridan da ya shafi kasuwanci da sanya hannun jari ya ce "A tsawon rayuwata abin da na fi tattaunawa da 'yan kasuwa, shugabannin kamfanoni da masu zuba hannayen jari shi ne faɗuwa, sai dai gabaɗaya abin da suke nuna mini shi ne faɗuwa wata aba ce da suka saba arangama da ita, kai wasu ma daga cikinsu abin da suke cewa shi ne da wahala su sanya hannun jari a wani abu ko bayar da kuɗi ga wani kamfani ko aiki da bai taɓa fuskantar rashin nasara ba."


Mamaki


Wani zai yi mamaki, shin ko ka san faɗuwa ita ce tushen nasara?, Eh tabbas faɗuwa wata aba ce da ke haɓaka cin nasara a rayuwa, tana bayar da damar gane kurakuran mu da kuma yadda za mu kiyaye sake aikata wannan abin anan gaba.


Bill ya taɓa cewa "Faɗuwa muguwar Malama ce, tana shagaltar da masu wayo cewa ba za su yi asara ba". Wata ƙila ba ka fahimta ba, to bari na gwada yi maka bayani, faɗuwa na sanya mutum mai wayo fahimtar me ya jawo,?,Ta yaya ya faru? Ta ya zai kiyaye gaba? A duk lokacin da ya yi rashin nasara, har ya zamana cewa ya gama fahimtar duk wasu dalilan da su ke sanya shi rashin nasara, daga nan kuma sai ya shagala cewa ba zai faɗin ba a duk lokacin da zai tunkari wani abu.


Eh, tabbas faɗuwa ba abar farin ciki ba ce lokacin da ka tsinci kanka a cikinta, kuma ba aba ce da za ka saki jiki da ita ba, ko yin sakaci kawai don ta faru da kai ba.


Sannan ya kan ɗauki wasu shekaru ko watanni kafin mu gane cewa ita ɗin babbar malama ce da ta ke koyar da mu darussa daban-daban na rayuwa, har wata rana mu ce wallahi gwara da abu kaza ya faru duk da kuwa a lokacin faruwar sa mun yi baƙin ciki da jimami, kuma na ba ka aiki, shin ko hakan ba ta taɓa faruwa da kai ba, ko wani a kusa da kai da har kai da kanka ka yarda gwara da wannan abin baƙin cikin ko asara ya faru da kai ko da shi ba?


Da akwai wani mutum da ya je wata tattaunawa domin samun aiki amma rashin E-mail ya sanya bai samu aiki ba, don haka sai ya fara sayen ƙwai da naira dubu ukun da ya rage masa, cikin sati uku sai da ya ninka kuɗin sau goma bayan buƙatunsa, a ƙarshe me ya faru? Sai da ya zama mai arziki tare da tarin kuɗaɗe, to shin da ya yi nasarar samun wannan aikin ya kake gani?


Jack ma mamallakin kasuwar yanar gizo mafi girma a duniya wato Ali Express ya nemi ayyuka daban-daban ba tare da ya samu nasara ba, a ƙarshe ya ƙirƙiri wannan kasuwar.


Kamfanin gyama-gyamai na Rovio sai da ya faɗi sau hamsin kafin ya samu nasara.


Bayan gagarumar nasarar kamfanin Apple sai kuma ya fuskanci faɗuwa har ya zamana cewa Steve Jobs da ya samar da kamfanin a 1985 an kore shi, wanda hakan ya sa ya yi ƙasa daga kamfani na ɗaya zuwa na can ƙasa, tattalin arzikinsa ya karye har zuwa farkon 1990s, sai gashi a shekarar 1997 Job ya dawo kamfanin kuma sai ga shi zuwa shekarar 2011 ba wai iya zamar da kamfanin ya yi wanda babu kamarsa ba, amma gabaɗaya ya kawo canje-canje a masana'antar fasahar computer, music, phones da sauran su, har ma ya taɓa cewa a 2005 cewa "Ban ga hakan ba a da, amma yanzu ya zamana cewa kora ta daga Apple shi ne mafi alherin abin da ya taɓa faruwa da ni"


Idan zan ci-gaba da jero maka tarin mutane da kamfanonin da suka faɗi kuma hakan ya zame musu alheri da sai na cika maka littafi da rubutu.


Amma, abu na ƙarshe da nake son ka fahimta a wannan rubutun shi ne tabbas faɗuwa ba abu ne da ake so ba, amma za ka iya amfani da ita wajen cin nasara a rayuwar ka fiye da a ce ba ka faɗi ba.


Wasu masu dabara a duk lokacin da za su fuskanci abu kamar gina kamfani, kasuwanci, karatu da sauran harkoki sukan mayar da hankali kan ƙalubale da rashin nasarar da wasu suka fuskanta a baya kafin su fara, har sai ya zamana cewa duk wani rashin nasara da aka taɓa samu sun karance shi kuma sun gano yadda za su kiyaye kansu, sai da kuma suka yi nasara, ba komai hakan ke ƙara musu ba, face ƙwarin gwiwa da jin cewa tabbas za su yi nasarar.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user