Friday, 6 December 2024

Yadda Matakin Farko Zai Sauya Rayuwar Ku

Tura Wannan Zuwa Ga

Wani mai hikima yake cewa "Ba ka buƙatar zama shahararre don farawa, amma kuma dole ka fara domin zama shahararre."


Yadda Matakin Farko Zai Sauya Rayuwar Ku
Hoto: Deposit photos

Marubuci:- Ibraheem Aleeyu


Haka zalika tafiyar dubunnan kilomita ana fara ta ne da taku ɗaya, matuƙar ba'a fara wannan taku ɗayan ba, shikenan duka sauran ma ba za' a yi su ba.


To shin me ake so ka fahimta a cikin wannan bayanin?


Fara wata tafiya, cimma wani buri, da kuma samar da duk wani sauyi mai amfani ga rayuwa zai iya zama wani abu da mutum zai yi ta zuwa ya kawo a kansa, amma babban ƙalubalen shi ne fara wannnan abin wanda kuma farawar shi ne abu mafi wahala, daga zarar ka fara sauran abubuwan da za su biyo duk za ka same su da sauƙi.


Bari na tambaya, shin sau nawa za ka ji kana jin kasalar yin wani aiki ko tafiya, amma da zarar ka fara sai ka ga komai ya zo da sauƙi?


Wata rana za ka ji kamar ba za ka iya taka ƙafar ka ba saboda gajiya, amma da zarar ka fara tafiyar, shikenan sai ka ji komai ya zama daidai.


To haka ma yake ga wani abu mai muhimmanci da kake son farawa, za ka ɗauki lokaci kana tunanin anya kuwa zan iya wannan abin? Ko kuma ka yi ta tunanin matsalolin da za su iya daƙile ka daga cimma ƙudirin ka, maimakon ka dinga duban amfani da kuma yadda za ka magance matsalolin sai ba kai ba, wanda hakan sai ya sa ka karaya ka kasa farawa, daga nan kuma shikenan ka faɗi, saboda dole dai sai ka fara kafin ka ci nasara.


To kamata ya yi ka tuna cewa "ƙwarin gwiwa ba shi ne rashin tsoro ba, amma shi ne kana jin tsoron abu ka tunkare shi". Kowanne kalar abu ne kawai buƙatar shi ne ka fara, koda ba ka shirya ba kuwa, don kuwa jiran cewa sai ka shirya ɗin nan shi ne ya ke jawo nawa/jinkiri (procrastination ), daga nan a mafi yawan lokuta koda mutum ya samu halin shiryawar sai kuma ya manta, ko kuma ya ƙara ba wa kansa wani uzuri na ƙin farawar.


Ka fara


Ka daina faɗar zan yi kaza da kaza kawai ka fara.


Ka fara koda ba ka shirya ba.


Wani ɗan wasan ƙwallon ƙafa ya taɓa cewa "Ƙwallon da kake da damar bugawa amma ka ƙi, to ka rasa damar cin nasara da kaso 100, amma idan ka buga bisa mamaki sai ka ga ka ci nasara.".


Haka zalika matakin farko dai shi ne ya fi wahala, matakin farkon kuma shi ne farawa, daga ka fara kuma duk sauran mai sauƙi ne.


Ka daina magana ka fara aiki.


Matakin farko shi ne mafi kyawun mataki.


Ka fara yanzu domin ka haskaka anan gaba.


Idan har kuna jin daɗin maƙalolin shafin nan namu, to ku hanzarta sanar da dukkan abokan ku ko ƙawayen ku da dukkan waɗanda ku sani, ku gaya musu sunan adireshin shafin nan namu domin su ma su shigo cikin shafin su dinga amfana da shi kamar yadda ku ma kuke yi a kullum a kyauta.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user