Friday, 20 December 2024

Yadda Za Ku Biya Bashi Ba Tashin Hankali

Tura Wannan Zuwa Ga

1. ADDU'A


Duk wata dabara ba ta fitar da mutum daga rikicin bashi ba tare da taimakon Allah ba. 


Bashi wata iriyar matsala ce wadda bayan ƙarfinka na zahiri har ƙarfin tunanin ka tana karyawa, sai mutum ya ji duk ba shi da kuzari, ko ya ji ya kasa aikata wani abu da zai kawo masa ci gaba a rayuwarsa saboda tunanin bashin da ake bin sa.


Yadda Za Ku Biya Bashi Ba Tashin Hankali
Hoto: Sergei Chuyko

Marubuci:- Abubakar Abba


Shi ya sa Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama ya koya mana wasu addu'oi domin fita daga matsalar bashi.


Daga cikin su akwai:


"اللهم أكفني بحلالك عن حرامك وأغننى بفضلك عنمن سواك" 


Akwai wasu addu'o'in masu yawa, wanda idan ka bincika su za ka same su kuma da taimakon Allah za ka ga komai ya zo da sauƙi.


Sannan a yawaita Istigfari, da Salatin Annabi, wannan kuwa babban makami ne na yaƙar damuwa da tashin hankali.


2.  LISSAFA NAWA NE AKE BIN KA BASHI, DA WANDA SUKE BIN KA BASHI


Anan za ka gane muhimmancin lissafi da rubutaccen lissafi, domin idan ba ka rubuta wanda suke bin ka bashi ba, da kuma adadin abin da suke bin ka ba, za ka shiga ruɗani sosai, domin ƙwaƙwalwarka za ta iya ba ka kunya wata rana.


Rubuta sunaye na wanda suke bin ka bashi zai sauƙaƙa maka wajen sanin hanyar da za ka ɓullowa kowa wajen biyansa.


Sanin yawan bashin da ake bin ka zai taimaka maka wajen sanin hanyoyin da za ka bi wajen biya da kuma sanin irin aikin da za ka yi ka biya su.


3. KA TSARA KASAFI NA KOWANE WATA


Fitar da tsarin abin da za ka kashe a wata, da daidaita shi yadda zai taimaka maka ka biya wani kaso na bashin da ake bin ka, zai taimaka maka sosai wajen samun sauƙin biyan bashin.


Idan ka zauna haka babu tsari, zai wahala gare ka ka iya biyan bashi.


Amma ka tsara kasafi na abin da kake buƙata a wata, da abin da kake tsammanin samu, da yadda za ka ƙara hanyar shigowar kuɗinka, da abin da ya kamata ka biya bashi duk wata, abin da ya kamata ka kashe a wata, da taimakon Allah hakan zai sauƙaƙa maka wajen samun mafita.


4. FARA BIYAN BASHIN DA YA FI MATSALA


Idan ana bin ka basussuka da yawa, zai zama ka shiga ɗimuwa, wataƙila ka rikice ka ce za ka biya kowa lokaci guda, wanda yin haka kuskure ne.


Abin da ya fi muhimmanci shi ne ka tsaya ka duba bashin da ya fi ba ka matsala, ko wanda zai iya jefa ka matsala a kusa, ko wanda ya fi ɗaga maka hankali ya hana ka sukuni ko wanda ya fi yawa kuma lokacin biyansa yake a kusa, kodai wani abu makamancin wannan, ka fara da shi ragowar za su zo maka da sauƙi, domin za ka samu nutsuwa da ƙwarin gwiwa bayan ka sallami bashin da yake ci maka tuwo a ƙwarya.


5. KA BIYA DAIDAI ƘARFINKA


Wasu da zarar an zo an matsa musu kan sai sun biya bashin da ake bin su, sai su ga gwara su biya nan take su huta, e hakan yana da kyau wani lokacin, amma a wajen ɗan kasuwa hakan zai iya zamar masa matsala gagaruma wadda za ta iya kai shi ga faɗawa wani bashin kuma.


A duk lokacin da ake bin ka bashi, yi ƙoƙarin biyan abin da za ka iya, a hankali har ka kammala biya, kar ka yi wa jarinka illa, kar ka yi wa kanka illa, wadda daga ƙarshe za ka faɗa wata rigimar da ta fi ta farkon.


6. RAGE KASHE KUƊI BABU DALILI


Idan ƙaddara ta sanya ana bin ka bashi, to ka yi ƙoƙari iya ƙarfinka ka ga ka sallami mutane.


Daga cikin hanyoyin da za ka bi shi ne ka rage kashe kuɗi babu dalili, da zarar ka ga mai kaza ko mai lemo ka ce za ka siya, ko da zarar maƙocinka ya sauya abin hawa kai ma ka ce sai ka sauya naka, ko da zarar shagon kusa da kai ya yi fenti kai ma ka ce sai ka yi, ko da zarar ƙawarki ta sayi kayan kitchen ki ce ke ma sai kin siya, duk irin wannan kashe-kashen kuɗin ba naka ba ne.


Dole ka tabbatar duk abin da za ka siya yana da wani amfanin da zai ba ka damar biyan bashi ko ya taimakawa kasuwancinka ya tsaya da ƙafarsa, ko abin da ya zamar maka dole sai ka siya domin rayuwa ta tafi yadda ya kamata.


7. KA CI BASHI ƊAYA MAI ƘWARI


Wato wani lokacin, masu ƙananun basussuka sun fi masu manyan bashi uzzurawa da matsawa mutum, idan tsautsayi ya sa ka ci bashin mutane daban-daban kuma suka uzzura maka, ka rasa yadda za ka yi ka biya su akan lokaci, to hanya mafi sauki shi ne ka ciyo wani bashin mai ƙwari wanda za ka biya su duka, kai kuma ka zo ka mayar da hankali wajen biyan wannan bashin da kaɗan-kaɗan.


Wani lokacin wannan ita ce hanya mafi sauƙi, domin za ta ba ka damar nutsuwa da kuma samun tartibiyar hanya ba tare da ka shiga uku ba.


8. NEMI WATA HANYAR ƘARIN KUƊIN SHIGA


Yawanci buƙatu ƙaruwa suke a yanzu, ware wani kuɗi domin biyan bashi yana da wahala sosai idan hanyar shigar kuɗinka ba ta sauya ba.


Kana samun dubu 30 a wata, ana bin ka bashin da kake biyan dubu 15 a wata, buƙatunka suna ƙaruwa duk wata, hakan zai jefa mutum cikin damuwa sosai.


Amma idan ka yi ƙoƙari ka samu wata hanyar da kuɗi zai ƙara shigo maka, za ka samu sauƙi.


Misali, kana sayar da Atampa a kasuwa, zai wahala ka ce za ka ƙara wata sana'ar ba tare da ta farko ta samu tasgaro ba. To amma yanzu zamani ya zo da abubuwa masu yawa da za ka iya ba tare da sun hana ka sana'arka ta farko ba.


Za ka iya Video Content wanda kake nuna inda kake sana'arka, kuma mutane za su kalla, kai kuma za ka samu 'yan kuɗaɗenka a Monetization.


Za ka iya shiga Crypto, amma fa ka tabbata ka koya, kar ka shiga da ka a zo a samu matsala, ba ruwana.


9. BA WA KANKA KYAUTA


Masana sun gano cewa duk lokacin da kake wani abu idan ka san cewa za ka samu wata kyauta ko karramawa ko wani lada a ƙarshensa, to ka fi bayar da himma.


Haka ma za ka yi idan kana biyan bashi, sakawa kanka wata kyauta da za ka ji daɗinta bayan ka biya wani kaso ko wani adadi na bashin da ake bin ka.


Misali, ka sanyawa kanka cin wani abu da kake matuƙar sha'awa amma saboda ana bin ka bashi ba ka iya saya ka ci, kamar a ce ka daina cin Naman Kazar da kake so saboda kana ƙoƙarin biyan bashi, to da zarar ka biya wani adadi, sai ka sayawa kanka Kaza ka more.


Yin hakan zai ƙara zaburar da kai wajen kula da kuma kiyaye lokacin biyan bashin.


Akwai wasu tarin hanyoyin da za ka bi wajen biyan bashin da ake bin ka, zamu tattaunasu da faɗi a nan gaba in sha Allah.


Ku yaɗa wannan don Allah, mutane da yawa suna cikin bashi amma ba su san yadda za su biya ba, za ka samu lada idan ka taimakawa wani ya fita daga matsalar bashi.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user