Nasara wata aba ce da kowanne Ɗan Adam ya ke son cimmawa, ita kuma nasara shi ne cimma manufofi ko burika da mafarkan rayuwar ka ko muradan rayuwarka.
Marubuci:- Ibraheem Aleeyu
Ga kowanne mutum yana da matuƙar muhimmanci a ce yana da wasu manufofi a wannan rayuwa, ta yadda cimma su zai samar masa da farin ciki da kwanciyar hankali, ga duk wanda ba shi da wata manufa za'a iya cewa kamar matafiyi ne ya bar garin su ba tare da sanin ma inda ya nufa ba, babu guzuri ba tudun dafawa, to shin ya halin wannan matafiyi zai kasance?
Sai dai kuma, a lokuta da dama, mutum ya kan kasance da manufofi da dama a rayuwa, amma sai ya gaza cimma su, ya kasance mai cike da burika da mafarkan cimmawa amma sai ka ga ya gaza cika su, to shin mene ne dalili? Ba komai ba ne dalili face rashin tsari, wanda ni da wasu da yawa daga cikin al'umma mu ke fuskanta, to shin me nake nufi a nan?
Wani marubuci ya ce "Da wanda ya ci nasara, da wanda ya faɗi burin su ɗaya ne, abin da kawai ya bambanta su shi ne yadda suka tsara cin nasarar tasu."
Scott Adams ya taɓa cewa "Buri da son cimma manufa na waɗanda ba sa nasara ne, amma kyakkyawan tsari na masu nasara ne".
Har yanzu dai ba ka fahimta ba.
Abin nufi a nan shi ne ba iya samun manufa da burika ne kaɗai ke nuna cimma nasara ba, amma bayan haka sai ka samar da jadawalin yadda za ka ci nasarar, ka rubuta shi, ka jajirce, ka bi komai daki-daki.
Sannan ka yi aiki tukuru wajen cimma wannan nasarar, wannan shi ne zai zamo tsani da zai ba ka damar isa ga ƙololuwar burin ka ba tare da ka sare ba.
Idan har kuna jin daɗin maƙalolin shafin nan namu, to ku hanzarta sanar da dukkan abokan ku ko ƙawayen ku da dukkan waɗanda ku sani, ku gaya musu sunan adireshin shafin nan namu domin su ma su shigo cikin shafin su dinga amfana da shi kamar yadda ku ma kuke yi a kullum a kyauta.