A yanzu dai muna iya cewa an fara sabawa da tattalin arzikin Tinubu, na janye tallafi daga abubuwan rayuwa na yau da kullum.
Bugu da ƙari kuma, ga sabuwar Naira mara karfin faɗa aji a kasuwa.
Sai dai da yawan mutane haƙuri kawai suka yi, tare da dangana cikin abin da Bahaushe ke kira da tsammanin warabbuka, ko kuma gamu ga Allah bawan sarki ya rasa doki.
Marubuci:- Bello Ado Hussaini
Amma fa akwai wasu abubuwa guda uku, waɗanda ka iya taimakon mutum wajen samun sauƙi, ko ma fita daga matsalar baki ɗayanta ta, tare da samun sabbin hanyoyin shigar kuɗi.
Waɗannan hanyoyi su ne kamar haka;
Daidaitawa
Wannan yana nufin karɓar yanayin da aka samu kai a ciki, tare da yarda cewa rayuwa da ma juyawa take.
Muhimmancin karɓar yanayi shi ne, yana ba da nutsuwar zuciya, yadda mutum zai tsai da hankalin sa, wajen neman mafita.
Dalili idan ka gaza karɓar yanayin da ka samu kanka, to za ka shiga ruɗani har ka faɗa wata rigimar kuma daban.
Rinjaye a kan matsi
Wannan shi ake kira da ɗaukar dama. Wato duk wani yanayi komai muninsa yana zuwa da wasu damarmaki a cikinsa.
Lokacin da Boko Haram ta ɗaiɗaita Maiduguri, sai ƙungiyoyin agaji suka samu dama wadda ba su taɓa samu ba, wajen karɓar kuɗaɗen agaji da kuma ayyukan jin ƙai.
Hakan kuma na nufin baya ga aikin lada, annobar ta ba su aikin yi da samun alawus mai kauri ba Dollar.
A baya bayan nan, lokacin da gwamnati ta rufe kasuwanni, bayan zanga-zangar matsin tattalin arziki, sai 'yan kasuwa suka yi amfani da wannan damar wajen ƙarin farashin kayayyaki.
Wannan kaɗan ne daga misalan ɗaukar dama cikin lokuta ko yanayi na matsi da damuwa.
Kada kuma wani ya ce ana koyawa mutane rashin tausayi, a'a haka sunnar rayuwa take, musamman ta kasuwanci, ko ka yi ko a yi maka.
Sassauci
Wannan na nufin ka gane cewa idan kiɗa ya sauya, to rawa ma sauyawa take. Ma'ana ka kasance kana bin rayuwa yadda ta zo, maimakon ƙoƙarin tafiyar da ita cikin salo na bai ɗaya, koda kuwa yanayin bai dace da tsohon yanayi ba.
Da yawan waɗanda suka fahimci haka yanzu za ka ga suna tantance inda ya kamata su yi amfani da motocin su, da kuma inda za su je su hau Ɗansahu kamar kowa.
Hatta mutanen da ba su da isasshiyar solar a gida, za ka ga sun samo ƙananun fitulu na solar masu sauƙin kuɗi, maimakon kunna Generator.
Haka zalika wasu ƙananan hanyoyin samun kuɗi waɗanda a baya ba su kulawa da su, yanzu za ka ga ba'a wasa da su.
Sai ka aje girman kai, ka je ka buga ƙaramar harka ta ƙananun kuɗi, ka ɗura a aljihunka.
Waɗannan hanyoyi, idan an bi su za'a samu sauƙin rayuwa, har ma da samun ƙarin kuɗin shiga, nutsuwar zuciya da kuma ci-gaban rayuwa.
Allah ya ba mu dacewa Amin.