Akwai sao’i 168 a mako. To za ka shafe misalin sa'o’i hamsin kana aiki, sannan 56 kana bacci, hakan ya bar ka da misalin sa’o’i 60 domin yin sana’a.
Marubuci: Bello Galadanchi
Ka ga wannan adadi na lokaci ya ishe ka bai wa mara ɗa da mahassada kunya, saboda za ka iya ba da ƙwazo da himma ga aikinka na ofishi da sana’a, sai dai kuma dole ne ka koyi saka ƙafafunka a takalma daban-daban idan har kana so ka yi nasara.
Gargaɗi
Dole ne ka raba aikinka na ofishi da sana’a. Kar ka kuskura ka yi wani aiki na sana’a yayin da kake ofis, kamar zance, ko aika saƙonni, ko ciniki da sauransu.
Sannan kuma kar ka kuskura ka yi amfani da kayan ofishi a sana’arka, idan kuwa ba haka ba, za’a iya amfani da lauyoyi wajen ƙwace sana’arka, ka ga an-yi-ba’ayi-ba kenan.