FARGABAR FARA SANA'A
Tabbas mutane da dama tsoro da fargabar wani abu mara kyau yana hana su fara wani abu muhimmi a rayuwarsu. Wanda suke so za su fara sana'a sau da yawa suna fuskantar tsoro kala-kala.
Marubuci:- Abubakar Abba
Wasu na tsoron wataƙila mutane ba za su so sana'ar da za su fara ba?
Wasu na tsoron ta yaya ma za su samu kwastomomi?
Wasu na tsoron abin da mutane za su ce a kansu saboda sun fara wata sana'a.
Wasu kuma tsoronsu shi ne; idan sun fara sana'a ƙarshe jarinsu zai karye.
Wasu fargabar su shi ne, ta ina ma za su fara?
Wasu ma ba su san takamaimai abin da suke tsoro ba, su dai kawai suna fargaba kuma sun kasa shawo kanta.
Waɗannan tsorace-tsorace dama wasu wanda ba mu ambata ba, suna nan suna damun mutane da dama, kuma hakan ya hana su fara abubuwan da za su amfane su a rayuwarsu.
Idan kana fama da irin wannan matsalar, akwai hanyoyin da za ka bi domin shawo kanta, kuma da taimakon Allah za ka samu damar fara sana'ar da kake so cikin nasara.
1. KA RUBUTA NAU'IN SANA'AR DA ZA KA FARA
Duk lokacin da kake so ka fara wata sana'a ka yi ƙoƙari ka rubuta duk abin da ya zo ƙwaƙwalwarka a lokacin.
Rubuta nau'in sana'ar da za ka fara zai taimaka maka wajen fahimtar inda za ka dosa a gaba.
2. INA ZA KA DINGA SAMUN KAYAN AKAN SARI
Idan wani kayan za ka dinga sayarwa, ka nemi ina ne ake zuwa a sayo kayan akan sari, hakan zai taimaka maka wajen lissafin farashi da riba.
3. A INA ZA KA SIYAR DA KAYANKA?
Ka rubuta gurin da kake tunanin cewa ya dace ka yi sana'ar a wajen, a shagon kasuwa ne, ko a gida ne, ko a Online ne? Duka waɗannan abubuwan da ya kamata ka rubuta ne domin za su rage maka wahalhalu da fargabar abin da zai zo a gaba.
4. SU WANE NE KAKE SO SU SAYI KAYANKA? (TARGET CUSTOMERS)
Duk abin da za ka sayar ko za ka sarrafa, yana da kyau ka yi lissafin su wane ne za su saya idan ka fito da shi?
Hakan zai taimaka maka wajen farashi da kuma talla.
Za ka fita daga rigimar masu cewa kayanka ya yi tsada, ko masu cewa ba lallai ne kayanka suna da kyau ba saboda sun yi arha.
5. TA YAYA ZA KA TALLATAWA MASU SAYA?
Ka zauna ka yi iya tunaninka, wasu hanyoyi za ka bi domin tallata sana'ar taka idan ka fara, yin wannan tunanin zai taimaka maka wajen cire duk wani tsoro da fargabar abin da zai zo a gaba.
Rubuta irin wannan tsare-tsaren akan takarda zai taimaka ka daina tsoron fara wata sana'a kuma zai ƙara haskaka maka hanya domin za ka hango inda nasararka take da inda damarmakinka suke.
" Ba'a fafe gora ranar tafiya ".