Wednesday, 4 December 2024

Yadda Za Ku Yi Farin Ciki Ba Kudi

Tura Wannan Zuwa Ga

Farin ciki, walwala da kuma baƙin ciki, fushi ko damuwa duka ɗabi'u ne na zuciya, sai dai farin ciki shi ne abin da aka halicci zuciya a kansa (Natural emotion), kuma a kodayaushe shi ne abin da zuciya ke buƙatar kasancewa da shi, ma'ana dai mutum ya kan kasance kodayaushe a cikin yanayin farin ciki ba kamar baƙin ciki, da fushi ba da sai dai wani abu ya ratso daga nan sai ya katse farin cikin da kodayaushe ke tare da mutum, sai ka samu cewa mutum ya shiga cikin yanayin damuwa da rashin walwala, wanda ya ke cutar da zuciya ta ɓangarori da dama, ya sanya ta zafi, da ƙuna da sauran su.


Yadda Za Ku Yi Farin Ciki Ba Kudi
Hoto: Birmingham mail

Marubuci:- Ibraheem Aleeyu


Shi dai farin ciki masana da dama sun yi bayanin sa da cewa wani yanayi ne na jin daɗi, gamsuwa, da kuma cikar muradu, motsin zuciya ne (emotion) da ke biyo bayan abubuwa da dama, sai dai shi fa farin ciki ba wai kawai wani abu ne da ake buƙata na ɗan wani lokaci ba, zai iya zama wani yanayi mai tsayi ko ma na din-din-din.


Farin ciki fahimta ce, fahimta ita ce madubin da mu ke duban duniya da kuma bayaninta, da akwai mummuna haka zalika kyakkyawa, iya yadda mutum ya fahimci mene ne farin ciki iya yadda zai same shi, sau da yawa mutum sai ka ga kai a idon ka ya yi nasara idan kai ne kake a cikin yanayin da ya ke ciki za ka tsinci kanka a cikin matuƙar farin ciki, amma shi a wurin sa sai ka same shi yana cikin halin tsananin damuwa, da rashin walwala, watarana ma sai ya ji kamar ya kashe kansa kawai kuma duk akan wannan abinda kake ganin zai saka farin ciki, kuma shi da akwai wata fahimtarsa da ta sanya shi cikin wannan damuwar, haka zalika abu zai iya faruwa da kai wanda zai sanya ka damuwa amma a wurin wani ko ɗaya ba zai damu ba, zai ɗauki hakan a matsayin ba komai ba, da sauran misalai da dama, wanda ina da tabbacin idan ka yi la'akari da mutanen da kake rayuwa da su za ka gane hakan a aikace.


Tunda farin ciki abu ne da kullum ake son zuciya ta lazimta don kasancewar ta cikin lafiya. To shin ta ya za ka iya yin hakan? Amsar ita ce ta hanyar samarwa kanka da kyakkyawar fahimtar mece ce rayuwa, da kuma yadda za ka fuskance ta, me za ka tsammata a kodayaushe a cikin rayuwar ka, shin ta ya za ka yi hakan? 


Ta hanyoyi daban-daban kamar haka:


ƘARFAFAR KAI


A kodayaushe ka dinga ƙarfafawa kanka gwiwa, kada ka taɓa sanyawa zuciyarka tunanin abin da zai sare maka gwiwa, idan ka faɗi ka yi wa kanka kalaman ƙarfafa gwiwa, ka ƙaddara hakan a matsayin wani mataki na cin nasara, haka zalika idan ka yi nasara ka yi murna, ka yi farin ciki, kada ka taɓa kawo wani tunani da zai katse wannan farin ciki, ka yi tunanin cewa wannan ita ce iya ƙololuwar nasarar da za ka iya cimmawa, kuma ka cimma, ma'ana dai ta yiwu kana cikin wannan murnar wani zai iya kawo maka shakka a cikin wannan nasarar ta hanyar nuna gazawarka, ko nuna cewa ba ka yi komai ba, to kada taɓa la'akari da wannan.


GODIYA


A kodayaushe ya kamata ka kasancewa mai godewa Allah, a duk wani lamari da ya faru da kai ka tuna cewa Allah ya azurtaka da dubunnan abubuwan da suka fi wannan abin da ka rasa, ko ka kasa samu, ka dinga duba dubunnan mutanen da ba su da abubuwan da kai kake da shi ma'ana waɗanda ka fi, sai ka samarwa kanka da kwanciyar hankali, kada ka taɓa yin duba da waɗanda suka fi ka, ba za ka taɓa kwanciyar hankali ba, saboda a kullum sai ka gano waɗanda suka fi ka, a rayuwar ka da mutane, kada ka duba abubuwa marasa kyau da suka yi maka, ka yi duba da nagartattun abubuwan da suka yi maka, sai ka yi musu hukunci da su, a kullum ka dinga tuno abubuwa uku da Allah ya azurtaka da su, waɗanda su kaɗai sun isa yalwanta farin cikin ka, waɗannan kuma kowa ya na da su, a ƙarshe dai kodayaushe nasarar ka za ka dinga tunawa ba faɗuwar ka ba, tunani ɗaya za ka yi ga faɗuwa shi ne tunanin ɗaukar darussa daga gare ta.


KA JUYAR DA ƘALUBALE


Duk wani ƙalubale da ka yi karo da shi, to kada ya sare maka gwiwa, kuma ya saka ka damuwa, ka ɗauke shi wani mataki ne na koyo da kuma cimma nasara, sai ka tambayi kanka "Shin me zan iya koya daga wannan abin da ya faru da ni?" ko kuma "shin wanne ci-gaba zan iya samu ko ya kamata na samu a matsayina na mutum?"


NUTSUWA


A duk lokacin da wani abu da zai fusata ka, ko sanya ka baƙin ciki damuwa da rashin walwala ya faru, to ka lazimci nutsuwa a wannan lokacin, ka yi dogon numfashi ka yi murmushi, sannan sai ka fara ƙoƙarin mantawa da wannan damuwar, ka maida hankali kan abin da kake yi, da nemo duk wani abu da zai kawar maka da damuwa, da wani dalili da zai sa ka ga cewa wannan abin bai kai wanda zai sanya ka damuwa ba.


KYAUTATA MU'AMALA


Ka kyautata mu'amalarka da mutanen da kake tare da su, dangi, 'yan uwa da abokan arzika, kyakkyawar mu'amala da mutane wani ginshiƙi ne na samun farin ciki a rayuwa.


SAMAR DA MANUFA


Ya zama lallai ka samar da manufa a rayuwarka, a komai kake yi ya zamana da cewa da akwai wata manufa da kake son cimmawa, ta yadda idan ka cimma wannan manufar za ka samarwa da kanka farin ciki da nutsuwa a rayuwa, rayuwa ba tare da sanin dalili ba ya kan sa mutum ya tsinci kansa kodayaushe a cikin rashin nutsuwa, da yawaitar damuwa, amma ya zamana cewa a kodayaushe kana yin wasu ayyuka ne da kake so kake muradi za su taimaka maka gurin cimma manufofin ka, to za ka tsinci kanka a cikin damuwa da farin ciki.


SHAWARA TA ƘARSHE


A ƙarshe, farin ciki ba abu ne da ake samu haka kawai ba, ana da buƙatar aiki tukuru kafin samunsa, ba za ka zo kullum kana bacci ba ka da manufa da abinda za ka taimaki rayuwar ka da shi ba ka ce za ka yi farin ciki, ba za ka dinga biyewa zuciyarka kana yin faɗa da mutane ba, ka ce za ka yi farin ciki, ba za ka dinga zaluntar mutane ba ka ce za ka yi farin ciki, don kasancewar ka cikin farin ciki kana da buƙatar yin duk wani abu da zai sanya zuciyarka farin ciki kodayaushe, kana buƙatar aiki tuƙuru don cimma manufofin ka, rayuwa a kodayaushe ba aba ba ce da za ta zo maka a yadda kake so ba, sai ka kasance mai fuskantar ƙalubale, da tunanin yadda za ka mayar da ƙalubalen ka wani abu da nan gaba za ka yi addu'ar gwara ma da ya kasance, sai ka koya daga kurakuran ka, ka mayar da gazawarka nasara, sai ka yi farin ciki da duk nasarar da ka yi komai ƙanƙantar ta, kada ka tsunduma kanka a tseren ɓera, ta yadda za ka zama kai kodayaushe burin ka sai ka fi kowa a rayuwa, kada ka taɓa duban ababen da ka rasa, ka yi duba da waɗanda ka samu, kada ka taɓa tunawa da abubuwan da suka faru a baya, ka fuskanci yau ɗin ka, don gyara gobenka, wannan shi ne abun da zai dawwamar da farin ciki a rayuwar ka ko ba kuɗi, ya kuma ba ka damar fuskantar rayuwarka yadda ya kamata.


Idan har kuna jin daɗin maƙalolin shafin nan namu, to ku hanzarta sanar da dukkan abokan ku ko ƙawayen ku da dukkan waɗanda ku sani, ku gaya musu sunan adireshin shafin nan namu domin su ma su shigo cikin shafin su dinga amfana da shi kamar yadda ku ma kuke yi a kullum a kyauta.


Allah ya taimake mu Amin.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user