Sa'a (lucky) a rayuwa gaskiya ce, amma mafi yawan lokaci kafin ta yi amfani sai an yi ƙoƙari a kanta.
Marubuci:- Abubakar S. Wali
Saboda akwai sa'ar da lura ake da ita, akwai sa'ar da ƙirƙirar ta ake, kuma akwai sa'ar da amfani da aiki da ita ake.
Tambayar ita ce kai wacce irin sa'a kake nema a rayuwa?
Ga su kamar haka:
Sa'ar ɗabi'a
Ita irin wannan sa'ar ita take nemo mutum a duk inda yake saboda ɗabi'un ka, zubin tunanin ka (mindset) su za su saka wannan sa'ar ta gano ka.
Abun da kake buƙata wajen cin karo da wannan sa'ar shi ne ƙoƙarin zamowa gwani a cikin yin duk abun da kake yi. Ginawa kanka suna (branding) da kuma zamowa na daban a cikin yin abun da kake yi zai taimaka wajen haɗuwa da wannan sa'ar a cikin rayuwar ka.
Sa'ar kwatsam
Ita irin wannan sa'ar a rayuwa faruwa take kamar tsautsayi, wani lokaci mu kan kira ta da ƙaddara saboda faruwar ta ba shi da alaƙa da ƙoƙarin mu ko aikin da muka yi.
Ta yaya za ka samu irin wannan sa'ar?
Ita irin wannan sa'ar hanyar da za ka bi domin samun ta guda ɗaya ce: "Ka yi rayuwa kawai". Muddin kana rayuwa za ka ci karo da irin wannan sa'ar, saboda tana faruwa da kowa.
Sa'ar aiki
Ita irin wannan sa'ar ana samun ta ne a cikin yin aiki tuƙuru, jajircewa da maida hankali a cikin abun da ake yi.
Yadda wannan sa'ar take aiki shi ne: ƙoƙarin ka da himmar ka a wani abu za su taru su samar da damammaki (opportunities) masu yawa a cikin rayuwarka, ta yadda mutane za suke mamakin irin damar da kake samu a rayuwa.
Sa'ar Ganowa
Ita irin wannan sa'ar a rayuwa gano ta ake. Shirin opportunity spotting da Likitan Sana'a ya gabatar a shekarar da ta wuce abun da shirin ya fi maida hankali a kai shi ne gano wannan sa'ar ko damammakin da ke kewaye da mu.
Gano irin wannan sa'ar ƙwarewa (skill) ce da za ka iya koya. Idan kana so ka samu irin wannan sa'ar a cikin rayuwar ka sai ka koyi kallon al'amura da idon basira, ta yadda za ka iya gano sa'a har a cikin abun da ake gani ba sa'ar ba ne.