Friday, 6 December 2024

Zafafan Alamomi 19 Da Za Ku Gane Budurwa Ba Ta Son Ku

Tura Wannan Zuwa Ga

'Yan samari alamomin nan suna iya bambanta a gurin wasu 'yammatan, ya danganta da wayewa ko ilimi na budurwa ko garin su.


Zafafan Alamomi 19 Da Za Ku Gane Budurwa Ba Ta Son Ku
Hoto: Anetlanda/ISTOCK PHOTO

Marubuci:- Abubakar Usman


Wasu daga cikin alamomin da za su taimake ka wajen gane budurwa ba ta son ka ko ta daina son ka.


Kawai ka ƙyale ta ka nemi me son ka aboki da zarar ka ga alamomin nan.


Ga su kamar haka:


1. Idan matan gidansu ko ƙawayenta suna hirar ka suna faɗar kirkinka ita za ta dinga jin haushi, ko ta tashi daga gurin ko ta kama zumɓura baki ko hararar me faɗar maganar, wani lokaci har da faɗar baƙar magana.


2. Wata budurwar za ta dinga yawan tunani, a lokacin da kuke hira idan kai magana ta ce "Ina ji ba ka ce kaza da kaza ba". Ta ɗan faɗi kashi biyu cikin biyar na abun da ka ce ta yi shiru.


3. Kallon raini a fakaice, ko a ɗan fake ka a harare ka.


4. Idan ka tura a kira ta ba ta fitowa da wuri, kuma ba a ce maka tana wani abun ba kamar cin abunci, wanka, kwalliya da sauransu. 


Kuma idan ta zo ba ka ganin alamar sabuwar kwalliya, kuma ba ta ce maka "Masoyi ka yi haƙuri na ɓata maka lokaci, kaza da ka nake yi.". Kuma kullum haka take maka.


5. Wani lokacin kuna hira za ka ga tana wasan ta kawai.


6. Za ka ga sau da dama kana hira da ita ba ta sakewa ta yi hira sosai da kai, sai dai ka ji tana Umm, ehh, a'a, to, to ya zance ma da sauran su. Kuma ba wai rana ɗaya ba, ba kuma laifi kai mata ba, kuma ka san ita me surutu ce ba wai kunya ce ba, a'a ranaku da yawa idan kuna zance haka take yi maka.


7. Ba ta fiye damuwa da ta kira ka a waya ba, koda ɗan Please call me ko filashin ne, sai dai idan tana da wata buƙatar daban. 


Wannan ma shi ne ya fi baƙanta rai.


8. Ƙin ɗaukar wayar ka da wuri kuma koda tana kusa, kuma kusan kullum haka take.


Sannan ba ta faɗa maka dalili ba ko daɗaɗan kalamai ba ballantana ta nemi afuwar ka.


9. Idan ka ba ta abu ba ta nuna farin ciki balle ta yi godiya, ko ta ƙi karɓa tana me maka yanga


10. Ba ta fiya kula 'yan uwanka ko ƙannanka ba, koda a waya ne ta tambayi lafiyarsu ba ta yi.


11. Wata budurwar ma tana iya zagin ka ma a bayan idonka ko ta canja maka suna. Misali, wawana, sakaraina da dai sauransu.


12. Idan ta tashi fitowa gurin ka zance za ta zo ranta a ɓace, ba tare da ta fada maka dallin ɓata ran ta ba.


13. Idan ta fito wata har tsayuwar ta ma za ka ga kamar za ku yi faɗa da ita.


14. Idan ka nemi ka je gidan su ko ka aiko magabatan ka ba za ta yarda ba.


Kuma ba tare da wani dalili me ƙarfi da ta faɗa maka kan hakan ba.


15. Ba ta son kana yi mata maganar aure kamar ka ce watarana kin zama matata ko amaryata, balle ta ce maka mijina, ba za ta yi ba.


16. Ba ta damuwa da kai da harkokin ka.


17. Ba ta damu da ta dawo maka da Reply na SMS ɗinka ba, duk daɗaɗan kalaman da ka aika mata.


18. Idan kuna chating da ta ga ka hau Online ita za ta sauka, ko ta yi shiru ta ƙi like ko comment amma tana hira da wasu ko ka aika za ta ƙi kula ka, daga baya ta ce ba ta kai ko ta sauka bayan daga baya ta dawo.


19. Ba ta cika yin kwalliya idan ka zo ko a yaya take fitowa take, wata budurwar ma sai ta munanta kanta za ta fito don ka ce ba ka so.


Idan har kuna jin daɗin maƙalolin shafin nan namu, to ku hanzarta sanar da dukkan abokan ku ko ƙawayen ku da dukkan waɗanda ku sani, ku gaya musu sunan adireshin shafin nan namu domin su ma su shigo cikin shafin su dinga amfana da shi kamar yadda ku ma kuke yi a kullum a kyauta.


Gayu da fatan za ku kula, ku daina nacewa waɗanda ba sa son ku.


A kare mutunci da girma saboda tsaro.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user