Gaisuwa ga ma'abociyar mulkin adalci wadda ta mamaye zuciyata a bisa turbar adalci, wadda saboda ita idanuwana suka makance ga rashin ganin kyawun kowacce 'ya mace bayan ke.
Marubuci:- Mr. A. so
Ke kaɗai ce a raina, ina son ki masoyiyata abar farin cikin rayuwata.
Zan so ki kasance mai sani nishaɗi a yayin da nake cikin baƙin ciki.
Da fatan kina cikin ƙoshin lafiyya sirrin zuciyata. Gatana, uwar 'ya'yana abar ƙauna a gurina, ki kasance lafiya a koyaushe.
Kunnuwana ba su jin daɗin kowacce murya bayan taki.
Zuciyata tuni ta ce babu wata sarauniyar da za ta mulke ta da adalci bayan ke.
Zuciya ta amince da ki zamo uwar 'ya'yana.
Maganin baƙin cikin rayuwata ke kaɗai nake kallo na ji zuciyata ta samu sauƙi.
Ba abun da bakina yake son furtawa kamar irin kyakkyawan sunanki. Zan so ki kasance tauraruwa abar haskaka zuciyata a yayin da nake cikin bacci.
Idan har kuna jin daɗin maƙalolin shafin nan namu, to ku hanzarta sanar da dukkan abokan ku ko ƙawayen ku da dukkan waɗanda ku sani, ku gaya musu sunan adireshin shafin nan namu domin su ma su shigo cikin shafin su dinga amfana da shi kamar yadda ku ma kuke yi a kullum a kyauta.