Allah sarki Baby na yaushe ne mafarkina zai tabbata a kanki? Don so nake na gan ni dab da ke koyaushe.
Zafafan Gajerun Sakonnin So Zalla
Hoto: Dreams time
Marubuci:- Ridwan Khan Adam
Na yi miki tsantsar ƙauna tun kafin idanuwana su kalli daradaran idanuwanki mai ɗauke da launin fari sal da baƙi wulik.
Lokaci guda kallon hotunki ya kan sani nishaɗi.
Tunaninki kan haifar da jin daɗi a masarrafar sarrafa tunanin zuciyata.
Daga naki a kowanne lokaci mai rera baitocin ƙaunarki a kowacce daƙika.