Duk wanda bai taɓa yin kuskure ba, bai taɓa gwada wani sabon abu ba.
Babu maganin rigakafin wauta.
Kada ka saurari wanda yake da amsoshi,
saurari wanda ke da tambayoyi.
Marubuci: Saliadeen Sicey
Rayuwa kamar tuƙin keke ce. Don kiyaye ma'auni, dole ne ku ci-gaba da motsi.
Abin da ya fi jahilci hatsarin gaske, shi ne girman kai.
Kaɗan ne adadin waɗanda suke gani da idanunsu. Kuma suke ji da zukatansu.
Tunani aiki ne mai wahala; Shi ya sa kaɗan ne ke yin hakan.
Ban san da wane makaman za a yi yaƙin duniya na uku ba, amma za a yi yaƙin duniya na huɗu da sanduna da duwatsu.
Dalilin lokaci shi ne don kada komai ya faru lokaci guda.
Hanya mafi kyau don farantawa kanka rai, ita ce farantawa wani rai.
Duniya ita ce mafakar mahaukata ta duniya.
Ba za mu iya magance matsalolin yau da tunanin da ya haifar da su ba.
Kada ka taɓa raina jahilcin ka.
Duba Wannan Yanzu: Tarihin Rayuwar Albert Einstein A Takaice
Zaman Duniya akwai haɗari, ba don akwai mugaye ba, sai don mutanen da ba su iya yin komai ba.
Da zarar ka daina koyo, ka fara mutuwa.
Mai wayo yana magance matsala. Mai hankali ya guje ma ta.