Sunday, 8 December 2024

Zafafan Kalaman Kiran Waya Ga Budurwa

Tura Wannan Zuwa Ga

Lallai ba shakka son ki zai iya zama ajalina, musamman idan zuciya ta rasa ki babu makawa zan bar duniya da zanen hotonki a bangon zuciyata.


Zafafan Kalaman Kiran Waya Ga Budurwa
Hoto: Royalvectors/Vecteezy

Marubuci:- El-Nass


Kin shiga raina cikin rashin zato ko tsammanin zuciya, sakamakon damuwar rashin ki da ke cikinta ta zamo jigon da zai iya kai ta ga halaka.


A kullum sauraren sautin muryarki ne yake ƙara jefa ni cikin nishaɗi da farin ciki, domin na riƙe ki a matsayin makamin da zan yi yaƙi da shi a cikin duniyar masoya.


Komai rintsi komai wuya ba zan furta da-na-sanin soyayyata da ke ba domin na kan samun rahotan zato da tsammanin cewa soyayyata da ke alkhairi ce.


Ganin kyakkyawar fuskarki kan iya samar mini da warakar damuwa da baƙin cikin zuciya.


Ki yarda da cewa ina sonki. Kuma ba zan sauya ra'ayina ba koda so da ƙauna za su zama matsala a gare ni, ke ce ɗaya tilo.


A halin yanzu idan na rasa rayuwata son ki shi ne sanadi domin ina da tabbacin cewa girman soyayyarki zai iya haddasa mutuwar da za ta zama tarihi a cikin fadar masoyan asali.


Rayuwata da dukkan darasin da ke cikin ta suna a gare ki mallakar ki ce. Fatana ki riƙe ni amana.


Kyakkyawan lafazin bakin ki shi ne linzamin da ke janye ra'ayina wajen sha'awar zama kusa da wata 'ya mace.


Idan har kuna jin daɗin maƙalolin shafin nan namu, to ku hanzarta sanar da dukkan abokan ku ko ƙawayen ku da dukkan waɗanda ku sani, ku gaya musu sunan adireshin shafin nan namu domin su ma su shigo cikin shafin su dinga amfana da shi kamar yadda ku ma kuke yi a kullum a kyauta.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user