Monday, 2 December 2024

Zafafan Kalaman Soyayya A Lokacin Tsadar Rayuwa

Tura Wannan Zuwa Ga

Rayuwa ta yi wahala, abubuwa sun yi wuya yayin da komai ya yi tsada, amma duk da hakan cikin kowanne irin yanayi ba na sarewa da yawan begen ki.


Zafafan Kalaman Soyayya A Lokacin Tsadar Rayuwa
Hoto: Martin Vidal/Medium

Marubuci:- It'z Nazeephancy DH


Da ma ki aminta da ni ki sa ni a ɓarin daman ki na zamo koda hadimi ne a cikin fadar ki, lallai da na kasance mai yin aiki tuƙuru domin nuna biyayya ga umarnin ki.


Kowanne Ɗan Adam yana gusar da yunwar cikin sa ne da abinci, amma a gare ni murmushin fuskarki ne ke ƙosar da ni a lokacin da nake jin yunwa.


A lokacin da ban yi zato ba soyayyar ki da ƙaunar ki suka mamaye dukkanin wata gaɓa ta jikina. Musamman zuciyata wacce a halin yanzu ke ce mamallakiyar ta.


Ki so ni yadda na so ki, tabbas za mu bar tarihi a sansanin masoya masu soyayyar gaske da gaskiya har a dinga tuna mu a matsayin masoyan da babu kamar su a wannan zamanin.


Lalacewar komai dole akwai sanadi da dalili, to ni ina ganin sanadin mafarin lalacewar rayuwata shi ne rasa ki a matsayin abokiyar rayuwa.


Idan har kuna jin daɗin maƙalolin shafin nan namu, to ku hanzarta sanar da dukkan abokan ku ko ƙawayen ku da dukkan waɗanda ku sani, ku gaya musu sunan adireshin shafin nan namu domin su ma su shigo cikin shafin su dinga amfana da shi kamar yadda ku ma kuke yi a kullum a kyauta.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user