Wednesday, 25 December 2024

Zafafan Kalaman Soyayya Da Karamar Yarinya

Tura Wannan Zuwa Ga

Zarah ki ke cikin taurari, Sarauniya cikin Sarakuna haka Gimbiya kike cikin kuyangi. Ke daban ce ga komai, ƙaunarki ita ce jarina, na kan manta da komai na tuna ki.


Zafafan Kalaman Soyayya Da Karamar Yarinya
Hoto: Adobe Stock

MarubuciImran Musa Jahun


Amincin Allah ya tabbata a gare ki motsin zuciyata. Raunanniyar zuciyata ba za ta iya juriyar rashin ki a gare ni ba, babu wani daɗi da zai kai matsayin daɗin da zan ji idan kika kasance tare da ni ma'ana ki aminta da ni ki ce kina sona. 


Ƙunci ko damuwa ba ya hana ni ambaton haruffan sunayenki domin ko su ne mafi daɗi a gare ni a jerin sunayen 'yammata.


Kyawunki ya kai matuƙa ta yadda ba zan iya jeranta shi da dukkan wani kyau ba.


Rurutacciyar ƙaunarki ta cinye dukkan komai nawa, da sonki zuciyata ke rayuwa.


Na kamu da son ki a sa'ilin da ban yi aune ba, ina son ki, zan ci gaba da son ki har abada. Ke ce kawai a zuciyata, ke ce alfaharina, da ke nake a kodayaushe. Ki so ni.


Tsiron son ki ya yalwatu a ruhina a lokaci ɗaya da na kalli kyakkyawar surar jikin ki, kina da kyawun da duk wani ɗa namiji sai ya jinjina miki, ko cikin kyawawa ke ce Sarauniyar su. 

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user