Sunday, 1 December 2024

Zafafan Kalaman Soyayya Na Gargajiya Zalla

Tura Wannan Zuwa Ga

Wato yau da na tashi, sai na ga rana ta taso ta haske garin nan, amma duk hasken ta bai kai hasken fuskar da ya haske zuciyata ba, domin ni a zuciyata hasken fuskar ki abar ƙaunata ya fi duk hasken rana.


Zafafan Kalaman Soyayya Na Gargajiya Zalla
Hoto: Poem hunter

Marubuci:- Ridwan Khan Adam


Zuciyarki ta zama takarda, tawa ta zama biro na rubata miki shafin ƙauna.


Ki zama ƙofa na zamo makulli, mu haɗu mu buɗe ƙofar soyayyar lambun zuciyata.


Na kasa tsaye na kasa zaune a lokacin da na fara ganin ki a cikin taro, kin fita daban kamar wata a daren sha biyar.


Ki zama manfetur na zama inji mu haɗu mu tada lantarkin ƙauna.


Ya sahibata na ba ki filin zuciyata ki shiga ki yi shuka a duk wani lungu da saƙo na zuciya, ki shuka bishiyar so da ƙauna don mu samu inuwar da za mu shiga mu zauna mu yi soyayya.


Ke ce madubi abar dubawata duk safiya.


Kin zamo mini tamkar fetur a mota, rayuwata ba ke lami ce ya rabin raina.


Ke ce makwarariyar madarar zuciyata wadda da na sha za ta haskaka zuciyata ta yi fari.


Rayuwata babu ke tamkar wayar da babu caji ce, kuma babu layi, a mace ba amfani.


Kunnena ya kurmance saboda rashin jin kalaman ƙaunar ki kullum, ba ki ya daina magana daidai saboda rashin begen zumar rayuwata kullum.


Ya tsagwaron zallar tsabar ƙwayar tsokar zuciyata, idona zai makance saboda rashin ganinki a yau da kullum.


Ya gangariyar madarar zumar da ba ta da gauraye.


Ya tauraruwa a cikin jinsin taurari mai haske zuciyar masoyinta.


Idona ya buɗe ya ga haske irin na walƙiya don ya gan ki.


Zuciyata na shan lagwadar zuma da madarar ƙauna.


Ke ce lafazin rayuwata.


Alfijir na ƙauna ya keto, tsuntsayen soyayya sun tashi suna yawo a sararin samaniyar zuciyata.


Ya fankar da ke juya zuciyata, zan zamo kwale-kwale ki shigo mu hau kan kogin so.


Na zamo katifa ki zamo gado a cikin ɗakin ƙauna.


Hadarin begen ki ya haɗo, guguwar son ki ta taso, sai ruwa mai ƙarfi ake yi na ƙaunar ki a filin zuciyata.


Gaisuwa daga kamfanin so, harabar ƙauna, gida mai lambar zuciyata, layin begen ki, zuwa ga rabin rayuwata.


Ya majaujawar zuciya ta, zan zama guga ki zama igiya mu haɗu a jefa mu cikin rijiyar soyayya.


Ya tsokar zuciyata, zan so a ce ki zama fura na zama nono mu haɗu a ƙwaryar soyayya.


Ya sahibata ki zama fukafukin dama na zama na hagu mu haɗu mu tada tsuntsun soyayya.


Ya masoyiyata, ki zamo bishiya na zamo ruwan da zai ratsa ta ƙasar so ba don komai ba sai don na shayar da ke.


Ya masoyiyata, ki zamo hanta na zamo jini, mu ga mai raba tsakanin mu.


Ludayin ƙaunar ki ya mamaye mini ƙoƙon zuciyata.


Ya masoyiyata, ki zamo mai na zamo albasa mu haɗu mu soye juna.


Masoyiyata, ki zama kyandir na zamo ashana, ki zamo itace na zamo makamashi mu haɗu mu hura wutar so, domin mu tafasa tukunyar ƙauna.


Ya madarar zuciyata, ki zamo siminti na zamo bulo mu gina gidan ƙauna a filin soyayya.


Ya zare da allurar da ta ɗinken zuciyata, ba zan taɓa daina son ki ba har sai wutar lantarki ta zauna a Najeriya.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user