Ƙaunarki ce mafari kuma silar wanzuwar duk wani farin ciki ko haske a cikin duniyata, domin annurin amintacciyar zuciyarki ne mahaɗi ko na ce cikon farin cikin zuciyata a koyaushe.
Marubuci:- Yaron MLM KD
Hmm a duk lokacin da tattausan lafazinki ya tunkari ƙofar zuciyata da zummar isar da saƙon farin cikin da ke zuciyarki, sai na ji daddaɗan shauƙin da ruhina ya mallaka sanadin kamuwa da ƙaunarki ya zo tarbar shi a daidai gaɓar gangar jiki da kuma ruhina, haƙiƙa wannan ƙwaƙƙwaran dalilin shi ne mahaɗin ƙwarin gwiwar da ta sa nake ji a jikina ke ta musamman ce domin ba da iya zuciya kaɗai nake ƙaunarki ba, har da jin ki a raina ma.
Uhmm Allah sarki zuciyata haƙiƙa na kan ji tausayin kaina a bisa yadda na ga zuciyata tana rarraba aikin ƙaunarki izuwa sassan jikina, domin tun kafin a je ko'ina har na kai matakin da ba zan iya rayuwa babu ke ba.
Ina da tarin burika a cikin rayuwata amma mallakar zahirin mafarkin sace zuciyar kyakkywar gimbiyata shi ne rubutun da zuciyata ke iya karantawa a koyaushe, kuma shi ne karatun da bakina yake maimaitawa a yanzu haka.
Nauyin furuci ko faɗin cewar ke kyakkyawa ce ba'a iya wuyana kaɗai ya rataya ba, haƙiƙa wannan nauyin ya rataya ne a wuyan duk wanda ya samu nasarar yin tozali da kyakkyawar fuskarki. Bugu da ƙari ma a ce kin bayyana kyakkywan murmushin ki a lokacin.
Indai har zuciyata za ta iya samun farin ciki sanadin gani ko jin haɗaɗɗiyar lallausar muryarki, to mene ne zai hana zuciyata zumuɗin san kasancewa da ke? Ke ce wacce zuciyata ta sahalewa rayuwa da ita ta har abada. Saƙo daga naki sarkin soyayyar ki.
Idan har kuna jin daɗin maƙalolin shafin nan namu, to ku hanzarta sanar da dukkan abokan ku ko ƙawayen ku ko masoyan ku da dukkan waɗanda ma ku sani, ku gaya musu sunan adireshin shafin nan namu domin su ma su shigo cikin shafin su dinga amfana da shi kamar yadda ku ma kuke yi a kullum a kyauta.