Tuesday, 17 December 2024

Zafafan Sakonnin Rabuwa Da Masoyi Masu Sa Kuka Na Soyayya

Tura Wannan Zuwa Ga

Na kwaɗaitu da kasancewa tare da kai har ƙarshen rayuwata, amma sai dai kasancewar kai namiji ne wanda ya rasa gaskiya a cikin rayuwarsa ya sa ba za mu iya rayuwa tare ba.


Zafafan Sakonnin Rabuwa Da Masoyi Masu Sa Kuka Na Soyayya
Hoto: Voyagerix ISTOCK PHOTO

Marubuciya: Fatima


Ka yi haƙuri wannan ita ce fahimtata a kanka.


Na yi maka takaicin rasa gurbin da ka yi a cikin zuciyata, a yanzu zan iya cewa mun rasa juna kenan har abada.


Na zargi ƙaddara da laifin haɗa mutane biyu a guri ɗaya bayan ta san ba za su kasance tare ba har tsawon rayuwa, da ta kama haɗa mu alhalin ba za mu kasance tare ba.


Na yi burin ɗanɗana maka zumar da ke tattare da soyayyata amma sai dai ni da kai mun kasance wasu mutane ne masu mabambantan manufofi wanda hakan ya sa ba za mu taɓa rayuwa ƙarƙashin inuwa ɗaya ba.


A matsayina na jarumar da ta san kimar so da soyayya nake cewa mu kasance masu yi wa juna fatan alkhairi.


Cikin rayuwar soyayyar ka ta gaba, ina fata ka kasance mai gaskiya, sannan kuma mai girmama buƙatun masoyiyar ka muddin ba su saɓawa Shari'a ba.


Na gode sosai.


Sai watarana.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user